Miji Ya Shiga Mamaki Yayin da Ya Tarar Matarsa Na Wankin Bargo da Darduma a Kasar Waje
- Wani dan Najeriya ya shiga mamaki yayin da ya ga matarsa na sana’ar wankin darduma a wani gida a kasar waje
- A bidiyon da yadu a kafar TikTok, ya tambayi matar dalilin da yasa take wankin darduma a kasar waje a matsayin sana’a
- A martaninta, ta bayyana cikin farin ciki cewa, ana biyanta kudin da ya kai N203k kan kowanne darduma da ta wanke
Wata kyakkyawar mata da ke rayuwa a kasar waje ta bayyana wata sana’ar da ake samun kudade masu yawan gaske.
A wani bidiyon da aka yada a TikTok, an ga lokacin da take tsakiyar aikin wanke darduma mai datti, lamarin da ya dauki hankali.
Mijinta, wanda shi ma ya shiga mamakin ganinta a titi tana wankin ya cika da burin sanin dalilin yin wannan sana’a da take yi.
Matar ta bayyana cewa, ai wannan sana’a ce da ake samun alheri, domin ana biyanta kudin da ya kai N203,000 kan kowanne darduma da ta wanke.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mijinta ne ya dauki bidiyon lokacin da take wankin cikin farin ciki kana ya yada a kan kafar sada zumunta ta TikTok.
Kalli bidiyon anan:
Martanin jama’a bayan ganin mata na wankin darduma kan kudi N203k
Bayan ganin bidiyon, mutane da yawa ne suka bayyana mamaki da kuma bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin.
Wasu sun yi kokarin kwatanta kudin da kuma yadda darajar kudin Najeriya da kuma irin kokarin da ta yi na maida hankali kan abin da zai amfane ta. Ga kadan daga ciki:
@amlace223:
“200 Haa ya yi yawa mana.”
@taofeekaj75:
“Matar kirki kenan.”
@uniquebeauty1104:
“£200 daidai yake da 200+ a nijia.”
@quincey:
“Kenan idan kika wanke 5 za ki samu miliyan 1 kullum.”
Yadda mata ta kafta wa mijinta mari bayan ta gina gidaje biyu bai sani ba, ya tambayi dalili
A wani labarin, kunji yadda wata mata ta gina gidaje guda biyu ba tare da sanin mijinta ba, ya yi kokarin daukar mataki.
A lokacin da ya tambaye ta dalilin boye masa, sai kawai ta kafta masa mari don nuna matsanancin fushinta.
A rahoton, mijin ya bayyana gaskiyar abin da ya faru da kuma yadda suka samu sabani tun farkon lamarin.
Asali: Legit.ng