Majalisar Wakilai Za Ta Samar Wa Sarakunan Gargajiya Gurabe a Kundin Tsarin Mulki, Tajudeen Abbas
- Majalisar wakilan Najeriya za ta samar wa da sarakunan gargajiya rawar da za su riƙa takawa a kundin tsarin mulki
- Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas shi ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Zazzau
- Kakakin ya yi nuni da muhimmancin da masarautun gargajiya su ke da shi a cikin al'umma ya cancanci su samu gurbi a kundin tsarin mulki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, a ranar Asabar ya bayyana cewa majalisar za ta tabbatar da cewa sarakunan gargajiya sun samu rawar da za su riƙa takawa a kundin tsarin mulki.
Abbas ya bayyana cewa hakan ya zama wajibi ne saboda muhimmancin da sarakunan gargajiyan su ke da shi a cikin al'umma.
Jaridar Channels tv ta rahoto cewa kakakin majalisar ya bayyana hakan ne a fadar sarkin Zazzau, Mai martaba Nuhu Bamalli, lokacin ziyararsa ta farko zuwa Zaria a jihar Kaduna.
Abbas, wanda yake riƙe da sarautar Iyan Zazzau, shi ne yake wakiltar Zaria a majalisar wakilai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abbas ya yi nuni da muhimmancin masarautun gargajiya
A lokacin ziyarar da ya kai fadar sarkin na Zazzau, Abbas ya yi nuni da muhimmancin da masarautun gargajiyar su ke da shi inda ya yi kiran da a tuna da su a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan na shekarar 1999.
A kalamansa:
"A yau ina so na yi maka alƙawari. Na tuna kusan shekara uku da suka wuce lokacin da mu ka yi zama kan garambuwal na kundin tsarin mulki, ka yi magana kan buƙatar sarakunan gargajiya su samu rawar da za su riƙa takawa a kundin tsarin mulki.
"Ina son tabbatar maka da cewa yanzu muna da wannan damar. A yanzu ina a matsayin ɗan ka a kujerar kakakin majalisa, za mu sake yin duba akan wannan kuɗirin ta yadda sarakunan gargajiyarmu za su samu rawar da za su riƙa takawa a kundin tsarin mulki."
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bayyana Yadda Wani Yankin Najeriya Ya Yi Asarar N4trn Cikin Shekara Biyu Saboda Dalili 1 Rak
"Mun zo nan ne kuma domin neman haɗin kan masarautun gargajiya na Arewacin Najeriya da ƙasa gaba ɗaya. Muna son kuma ku bamu shawara kan yadda za mu samu nasara a shugabancinmu. Inda mu ka yi kuskure a gaya mana gaskiya. Ina neman goyon bayan Sarkin Zazzau da gaba ɗaya mutanen masarautar."
A na shi jawabin, Sarkin Zazzau ya bayyana cewa mafi yawan ƴan siyasa da sun lashe zaɓe sai su manta da masarautun gargajiya, cewar rahoton The Nation.
Sarkin ya buƙaci ƴan majalisar da su yi aikin kan ƙudirin domin amincewa da shi ba tare da wata jayayya ba.
Sanatoci, 'Yan Majalisa Za Su Kashe N40bn Kan Motoci
A wani labarin na daban kuma, Sanatoci da ƴan majalisar wakilai za su samu sabbin motocin hawa domin gudanar da ayyukansu.
Ƴan majalisun da za su kashe N40bn domin siyo motocin waɗanda dama a al'ada an saba yi musu hakan bayan an rantsar da su.
Asali: Legit.ng