Bauchi: Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 7, Sun Kwato Makamai

Bauchi: Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 7, Sun Kwato Makamai

  • Jami'an rundunar yan sandan jihar Bauchi sun cika hannu da wasu masu garkuwa da mutane bakwai da suka addabi al'ummar Alkaleri ta jihar
  • Yan sandan da suka kai samame mabuyar yan bindigar sun yi nasarar kwato muggan makamai iri-iri
  • An kuma kama wani dan fashi da suka farmaki wani dan achaba tare da sace masa babur bayan sun doke shi a kai

Jihar Bauchi - Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne su bakwai sannan ta kwato makamai guda hudu a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Kashim Shettima Ya Hadu Da Atiku Abubakar a Abuja

Jami'an yan sanda
Bauchi: Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 7, Sun Kwato Makamai Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wakil ya kuma bayyana sunayen wadanda aka kama a matsayin Isah Gambo, Hamza Ali, Ali Isyaku, Danlami Isyaku, Abubakar Isyaku Adamu Alhaji Lado, Usman Dan Asibi wanda aka fi sani da Na Mansur, dManukkaninsu yan kauyukan Mansur da Papa Yalo a karamar hukumar Alkaleri.

A cewar Wakil, jami'an rundunar yan sanda a hedkwatar Alkaleri tare da hadin gwiwar kwararrun maharba ne suka kama wadanda ake zargin yayin da suka kai samame wasu wurare masu hatsari a kauyen Babarko da ke yankin Pali da kauyukan Yalo Karekare Digare da Gwana tsakanin 10 da 13 ga watan Yuli.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kwato muggan makamai daga yan bindigar

Wakil ya yi bayanin cewa binciken farko ya gano cewa wadannan mutane da aka ambata sune kasurguman masu garkuwa da mutane da suka addabi al'umman Alkaleri da kewaye.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Yan Najeriya 4 Da Suka Yi Aiki Da Buhari Kuma Suka Samu Sabbin Mukamai

Ya kara da cewar an gudanar da bincike a mabuyansu mabanbanta sannan an gano wadannan haramtattun makamai: bindiga kirar revolver guda daya, bindigar AK-47 guda daya, wani karamin bindiga guda daya da kuma wani bindiga daya.

Yan sanda sun kama wani dan fashi a yankin Itas Gadau

Ya kuma bayyana cewa a wani aikin, an kama wani mai suna Munkailu Haruna, dan shekaru 22 a kauyen Gandiyel da ke karamar hukumar Itas Gadau kan zargin fashi da makami bayan korafin da wani Saleh Ahmadu na kauyen Ayas da ke karamar hukumar Jama'are ya shigar.

Ahmadu wanda ya kasance dan achaba ya ce a ranar 13 ga watan Yuli, wasu mutane biyu da bai sani ba sun hau babur dinsa mara rijista daga garin Juma'are zuwa makarantar koyon Larabci na Jama'are da ke wajen gari inda suka buge shi a kai da karfe.

Bayan nan sai suka yi awon gaba da babur dinsa, wanda shine ya kai ga kama wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Hallaka Wani Dan Kasuwa A Bauchi Bayan Sace Shi Ya Gagara

Babban kwamandan Boko Haram, Khaid Malam Ali, ya mika wuya a jihar Borno

A wani labari na daban, mun ji cewa wani babban kwamandan kungiyar ta'addanci na Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād wanda aka fi sani da Boko Haram, Khaid Malam Ali, ya mika wuya ga rundunar sojojin Najeriya.

Malam Ali ya mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai da ke yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas tare da babban mayakinsa, Bunu Umar a jihar Borno, zagazola Makama, shahararren masanin lamarin tsaro a tafkin Chadi ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng