Hotuna Sun Bayyana Yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Ya Hadu Da Atiku a Abuja

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Ya Hadu Da Atiku a Abuja

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya hadu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a babban birnin tarayya Abuja
  • Manyan yan siyasar kasar biyu sun hadu ne a wajen wani daurin aure da aka kulla tsakanin Mohammed (Ameer) Bunu da Ikramullah Jamal Arabi
  • Duk da banbancin da ke tsakaninsu, yan siyasar sun ajiye siyasa a gefe sannan suka yi musabaha cikin annashuwa da walwala kamar babu komai a tsakani

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya hadu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a wajen wani daurin aure a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli.

Wannan na daya daga cikin yan haduwar da jiga-jigan kasar biyu suka yi tun bayan da aka fara shari'a kan babban zaben 2023, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Yan Najeriya 4 Da Suka Yi Aiki Da Buhari Kuma Suka Samu Sabbin Mukamai

Atiku ya hadu Shettima a Abuja
Hotuna Sun Bayyana Yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Ya Hadu Da Atiku a Abuja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Atiku wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben yana kalubalantar nasarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wacce a karkashinta ne Shettima ya yi takara tare da shugaban kasa Bola Tinubu.

Atiku da Shettima sun ajiye siyasa a gefe a wajen wani daurin aure a Abuja

Sai dai kuma, yayin da suka hadu a wajen daurin auren Mohammed (Ameer) Bunu da Ikramullah Jamal Arabi, su dukka biyun sun jingine siyasa a gefe sannan suka gaisa cikin raha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku da Shettima a wajen daurin aure a Abuja
Hotuna Sun Bayyana Yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Ya Hadu Da Atiku a Abuja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daga cikin wadanda suka halarci daurin auren wanda ya gudana a masallacin Al-Nur da ke babban birnin tarayyar kasar sun hada da tsohon mai ba kasa shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya, tsohon ministan sadarwa, Farfesa Ali Isa Pantami da sauran manyan masu fada aji.

Kara karanta wannan

Jerin Shahararrun Yan Siyasa Da Suka Ki Amsar Tayin Zama Ministocin Shugaban Kasa Tinubu

Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Tsige Shugaba Tinubu

A wani labari na daban, Legit.ng ta kawo a baya cewa kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben shugaban ƙasa ta jingine hukuncin da zata yanke zuwa ranar zama na gaba da zata sanar nan gaba kan ƙarar da jam'iyyar APM ta shigar.

A ƙarar da ta shigar, jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta roƙi Kotun ta rushe zaben da ya bai wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da Kashim Shettina nasara a watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng