Dokar Zaman Gida: Yankin Kudu Maso Gabad Ya Yi Asarar N4trn Cikim Shekara Biyu, Benjamin Kalu
- An yi kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki a yankin Kudu maso Gabas da su haɗa hannu wajen tarwatsa zaman gidan dole da IPOB ke sanya wa a yankin
- Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, shi ne ya yi wannan kiran ranar Juma'a wajen wani taro a jihar Legas
- Kalu ya bayyana cewa zaman gidan gidan da IPOB ta ƙaƙaba ya sanya yankin ya yi asarar N4trn a cikin shekara biyu
Wasu bayanai da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya fitar sun bayyana cewa kasuwanci a yankin Kudu maso Gabas ya yi asarar N4trn a dalilin zaman gidan dole da ƙungiyar ƴan aware ta IPOB ta ƙaƙaba a yankin.
Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, mataimakin kakakin majalisar bai bayyana inda ya samu waɗannan bayanan da ya fitar ba.
Kalu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli a wajen wani taro da aka shirya a jihar Legas.
A cewar jaridar Daily Sun, Kalu ya bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba zai yiwu mu fasa ayyukan kasuwancin mu ba. Dokar zaman gida a rsnar Litinin ta janyo asarar N4trn a yankin Kudu maso Gabas a shekaru biyu da suka gabata a cewar bayanan ƙididdiga."
Ya bayyana cewa zaman gidan ya janyo harkokin shigo da kaya da fitar da su zuwa sauran yankunan ƙasar nan sun samu tawaya.
Kalu ya bayyana cewa hakan zai shafi wasu yankunan ƙasar nan da su ka dogara da yankin wajen samar da wasu kayayyakin.
Kalu ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su shiga cikin lamarin
Ya buƙaci masu ruwa da tsaki a yankin da su haɗa kansu wuri ɗaya su samar da mafita kan wannan annobar da ta addabi yankin domin kasuwancin yankin ya haɓɓaka.
Gwamnan PDP Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Yadda Jiharsa Ke Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litini Saboda Abu 1
Jihohin yankin Kudu maso Gabas da dokar zaman gida ta shafa sun haɗa Abia, Anambra, Enugu, Imo da Ebonyi.
Dokar zaman gidan dai ta daɗe tun lokacin da aka cafke shugaban ƴan awaren IPOB Nnamdi Kanu.
Gwamna Mbah Ya Bayyanar Asarar Da Jiharsa Ke Yi a Dalilin Dokar Zaman Gida
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana irik asarar da ake tafkawa a jiharsa a dalilin dokar zaman gida.
Peter Mbah ya bayyana cewa duk ranar Litinin ana asarar N10bn a dalilin dokar zaman gidan da ƙungiyar ƴan awaren IPOB ta ƙaƙaba a yankin Kudu maso Gabas.
Asali: Legit.ng