Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta

Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta

  • An sha yar dirama a jami'ar ABU yayin da matashi ya nemi auren lakcararsa mace a bainar jama'a
  • Malamar ta fashe da kukan murna yayin da ta amsa tayin dalibin nata cike da so da kauna, inda sauran mutane suka dungi karfafa mata gwiwa
  • Lamarin da aka nada a bidiyo ya haifar da martani a soshiyal midiya, yayin da mutane da dama suka bayyana ra'ayoyinsu kan yanayin malamar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dalibin Najeriya, Big Bantin, ya haddasa cece-kuce yayin da ya nemi auren lakcararsa mace a cikin makaranta.

Lamarin ya afku ne a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya kuma ya haddasa cece-kuce a tsakannin masu amfani da soshiyal midiya.

Dalibi ya nemi auren malamarsa
Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta Hoto: @skidx_4real
Asali: TikTok

Bantin, mai rubuta waka da kade-kade, ya tunkari inda take zaune sannan ya gabatar mata da furanni. Mutanen da ke wurin sun yi ta kururuwa cikin farin ciki, suna masu kira ga malamar da ta amsa tayinsa.

Kara karanta wannan

“Yanzu Na Mallaki Gidan Kaina”: Budurwa Ta Ginawa Kanta Karamin Gida a Shekaru 19, Hotunan Sun Yadu

Da take karbar abun hannu bibbiyu, malamar ta fashe da kukan murna sannan ta rufe fuskarta a cikin tafin hannunta kafin ta karbi furen daga hannun matashin. Bidiyon ya yadu a TikTok. Legit.ng ta tattaro cewa duk don jin dadi ne amma ba wai neman aure na gaske bane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da take martani ga bidiyon, cikin barkwanci malamar ta bayyana cewa furannin na roba ne sannan ta umurci matashin da ya zo ya karbi abun sa.

"Roba ne ma....Ka zo ka dauki furannin robanka faaaa," lakcarar mai suna Ella Baliat ta rubuta."

Bantin ya amsa mata da wani sako.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Ayoola0163 ya ce:

"Zo ka gwada shi da iya salami fr kp… Ina mutanena na slt."

charlesunegbu1 ya ce:

"Saboda kana son guje ma 'carry over' koooo..namijin duniya."

Kara karanta wannan

“Ba Zan Daura Auren Nan Ba: Fasto Ya Yi Watsi Da Ma’aurata a Ranar Aurensu, Ya Fadi Dalili a Bidiyo

bossbrown ya ce:

"Ka nemi auren lakcararka hmmm baaba ba za ka sake faduwa jarrabawa ba, shawara mai cike da hikima."

The Joker ya ce:

"Ka ci darasinta ko bayan ka kammala karatu za ka ci gaba da cin jarraawar."

Airkabs the digital ancestor ya ce:

"Za ka iya neman aure ne idan kuna soyayya, shin hakan na nufin suna ta fita tare."

Fasto ya ki daura auren wasu masoya bayan an taru, ya fadi dalili

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani taron daurin aure ya dauki sabon salo na bazata lokacin da faston da zai daura auren ya fice daga wajen.

Yayin da yake nuna rashin amincewarsa, faston ya bayyana matsayin zaman angon a kasar a matsayin dalilinsa na kin daura auren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel