“Soyayya Ruwan Zuma”: Abokai Sun Yi Amfani Da Bari Wajen Tuka Amarya da Ango Zuwa Wajen Biki

“Soyayya Ruwan Zuma”: Abokai Sun Yi Amfani Da Bari Wajen Tuka Amarya da Ango Zuwa Wajen Biki

  • Wani bidiyo da ya yadu ya nuno lokacin da aka tuka wani ango da amaryarsa zuwa wajen bikinsu a cikin baro
  • Angon da amaryarsa sun hau kan baron sannan wasu matasa suka taru suka tuka su har zuwa wajen daurin aurensu
  • Bidiyon ya haddasa cece-kuce yayin da mutane suka yi kokarin fahimtar auren da yadda aka yi jigilar ma'auratan

An sha yar dirama yayin da aka tuka wani ango da amaryarsa zuwa wajen daurin aurensu a cikn baro.

Ba a san dalilin da yasa amaryar da angon suka zabi a yi jigilarsu zuwa wajen daurin aurensu a cikin baro ba, amma dai alamu sun nuna lallai sun ji dadin hakan domin dai sun kasance cikin farin ciki da annashuwa har zuwa wajen.

Amarya da ango sun isa wajen bikinsu a baro
“Soyayya Ruwan Zuma”: Abokai Sun Yi Amfani Da Bari Wajen Tuka Amarya da Ango Zuwa Wajen Biki Hoto: TikTok/@shenani568.
Asali: TikTok

Bayan daurin auren, amaryar, Shenani ta zakulo bidiyon domin mutane su kalla a TikTok.

Kara karanta wannan

“Kana Da Karfin Hali”: Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta a Bidiyo

A cikin bidiyon, an gano amaryar da angon a cikin wani baro da aka yi ado da kwalliya. Angon ya sanya riga da wando inda ya ci zanzaro yayin da ita kuma amaryar ta ci doguwar riga fari irin na amare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su duka biyun sun zauna ne a bayan baron yayin da mutane biyu ke tuka su da dukka karfinsu.

Wasu mutane da dama sun bi su daga baya, yayin da wasu suka riga su zuwa yayin da suke tattaki zuwa wajen bikin.

Abun mamaki, amaryar na ta murmusawa yayin da suke ci gaba da tattakin. Sai dai kuma a wani bidiyo na daban, amaryar ta wallafa wani fosta wanda a ciki aka yi wa auren da auren shagube. Ba a san ko da gaske auren suka ba tunda dukkaninsu matasa ne sosai.

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

“Ba Zan Daura Auren Nan Ba: Fasto Ya Yi Watsi Da Ma’aurata a Ranar Aurensu, Ya Fadi Dalili a Bidiyo

Jama'a sun yi martani

@charlestete1 ya ce:

"Ya yi kyau aure mafi kyau a duniya."

@user9975038735615 ya yi martani:

"Abun da ya fi muhimmanci shine cewa ka yi aure."

@joyjazzly ta ce:

"Nagode sosai yar'uwa. Wannan shi ake kira da so."

@TONY CRUZ ya yi martani:

"Na rantse wannan auren zai yi karko."

Dalibi ya nemi auren malamarsa a bidiyo

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dalibin Najeriya, Big Bantin, ya haddasa cece-kuce yayin da ya nemi auren lakcararsa mace a cikin makaranta.

Lamarin ya afku ne a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya kuma ya haddasa cece-kuce a tsakannin masu amfani da soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng