Cire Tallafi: Gwamna Nwifuru Ya Kara Wa Ma'aikata Albashi a Jihar Ebonyi
- Gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar APC ya ƙara wa ma'aikatar jihar Ebonyi albashin domin rage masu raɗaɗin cire tallafin mai
- Haka nan gwamna ya amince a ɗauki sabbin ma'aikata sama da 1,000 domin cike giɓin da ke akwai a ɓangaren ma'aikatan jihar Ebonyi
- Ya kuma umarci sakatariyar gwamnati ta duba yanayin harkokin kuɗin jami'ar jiha domin sanin halin da take ciki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ebonyi state - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da ƙarin albashin naira N10,000 ga kowane ma'aikacin jiha ba tare da la'akari da matakin aiki ba.
Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kai na jihar, Jude Okpor, ne ya bayyana haka ga manema labarin yayin da yake karin haske kan abinda aka tattauna a taron majalisar zartarwa.
Mista Okpor ya kuma bayyana cewa gwamnan ya aminta da ƙara ɗaukar sabbin ma'aikata 1,454 a faɗin kananan hukumomin jihar da ke shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.
Tribune ta rahoto Kwamishinan na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"An kawo batun albashin ma'aikata a taron kuma majalisar ƙarƙashin jagorancin shugaba mai girma gwamna ta amince da ƙara naira N10,000 a albashin kowane ma'aikaci domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur."
"Haka nan kuma majalisar ta amince da ɗaukar sabbin ma'aikata 1454 domin cike guraben da aka rasa tsawon shekaru a ɓangaren ma'aikatan jihar Ebonyi."
Bugu da ƙari, mambobin majalisar sun umarci sakatariyar gwamnatin jiha da ta sake nazari da bitar kashe-kashen kuɗin jami'ar jihar Ebonyi.
A rahoton Independent, ya ƙara da cewa:
"Bayan haka gwamna ya umarci SSG, Farfesa Grace Umezuruike ta duba harkokin kuɗin jami'ar EBSU domin sanin nawa suka shigo kuma nawa suka fita wanda zai taimaka wajen kasafin da za a rika ware wa jami'ar."
A ranar rantsuwar kama aiki 29 ga watan Mayu, 2023, shugaban kasa, Bola Tinubu, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba zata sake biyan tallafin mai ba.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Mai Martaba Oba Na Benin a Aso Rock
Wani rahoto na daban ya nuna cewa Oba na Benin mai martaba Ewuare II ya ziyarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock ranar Jumu'a.
Har kawo yanzun babu cikakken bayani kan dalilin wannan ziyara da babban Sarkin ya kai wa shugaban kasa amma ana hasashen ya je taya shi murna ne.
Asali: Legit.ng