Cire Tallafi: Abba Gida Gida Ya Soki Tinubu Kan Tsarin Rabon Kudi, Ya Bayyana Matsayar Shi A Kai

Cire Tallafi: Abba Gida Gida Ya Soki Tinubu Kan Tsarin Rabon Kudi, Ya Bayyana Matsayar Shi A Kai

  • Gwamnatin jihar Kano ta caccaki tsarin Shugaba Bola Tinubu na ba da tallafi don rage radadin da jama'a suke ciki
  • Tinubu ya ware N500bn don rage radadi bayan cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi yayin bikin rantsarwa
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce babu adalci a yanayin yadda aka tsara ba da tallafin inda ya ce Lagos kadai za ta tafi da kashi 47

Jihar Kano - Gwamnatin jihar ta soki tsarin ba da tallafin da Shugaba Tinubu ya ke shirin yi na N500bn.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli a Kano.

Cire Tallafi: Abba Gida Gida Ya Soki Tinubu Kan Tsarin Rabon Kudin
Gwamna Jihar Kano, Abba Gida Gida Ya Soki Tinubu Kan Tsarin Rabon Kudade, Inda Ya Ce Babu Adalci A Ciki. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Abba Gida Gida ya soki yadda tsarin rabon tallafin ya ke

Ya ce babu adalci a rabon inda jihar Lagos za ta kwashe kashi 47 sai yankin Kudu maso Kudu da kaso 17, inda sauran yankuna za su kwashi abin da ya rage.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ya ji tausayin talaka, gwamnan APC ya kara albashin ma'aikata saboda tsadar fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Gida Gida ya bayyana haka da rashin adalci da saba doka inda ya bukaci 'yan majalisa da su dauki matakan gyara a kan haka, Tori NG ta tattaro.

Idan ba a mantaba, Shugaba Bola Tinubu ya ware N500bn don rage radadin cire tallafi da gwamnati ta yi a ranar 29 ga watan Mayu yayin bikin rantsarwa.

Abba Kabir ya ce sun himmatu wurin rage karfin talauci a jihar

Gwamnan Abba Kabir Wada ya samu wakilcin mataimakinsa, Aminu Gwarzo ya bayyana himmatuwar gwamnatinsu na rage radadin talauci a kasar.

A cikin wata sanarwa da kakakin mataimakin gwamnan, Ibrahim Shu'aibu ya fitar ya bayyana amfanin kungiyoyin hadin gwiwa a bangaren kawo ci gaba da inganta rayuwar al'umma, cewar gidan talabijin na Channels.

Shugaban kungiyoyin a jihar Kano, Musa alkawa ya bayyana gudunmawa da kungiyoyin hadin kan ke bayarwa da inganta mambobinsu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Dattijon Arewa, Yakasai Ya ba Gwamnatin Abba Gida-Gida Shawarwari

Cire Tallafi: ’Yan Najeriya Sun Kushe Shirin Tinubu Na Raba N8000

A wani labarin, 'Yan Najeriya sun koka kan yadda tsarin rabon kudi da Shugaba Tinubu don rage radadin cire tallafi.

Tun bayan cire tallafin mai din, 'yan Najeriya sun sha fama da wahalhalu na tsadar man fetur.

Dalilin haka, shugaban ya ware N500bn don rage wa mutane radadi inda za a ba wa gidaje 12m kudi N8,000 na watanni shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.