"Ku Mika Wuya Ko Mu Tura Ku Lahira" Rundunar Soji Ta Aike da Sako Ga Yan Bindiga

"Ku Mika Wuya Ko Mu Tura Ku Lahira" Rundunar Soji Ta Aike da Sako Ga Yan Bindiga

  • Rundunar sojin Najeriya ta buƙaci yan ta'adda da yan bindigan daji su gaggauta fitowa daga dazuka su miƙa wuya
  • Kwamandan dakarun sashi na 8 a Sakkwato, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya ce ba zasu tsaya zaman sulhu da 'yan bindiga ba musamman a Arewa
  • Ya ce sojoji zasu ci gaba da kai samame maɓoyar 'yan ta'adda suna murƙushe su matuƙar ba su aje makami ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara - Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta yi kira ga 'yan ta'adda da 'yan bindigan jeji musamman a shiyyar Arewa maso Yamma su gaggauta miƙa wuya tun da wuri.

Rundunar sojin ta jaddada cewa ba bu zancen zama teburin sulhu da gurɓatattun mutanen da su ka zama barazana ga zaman lafiya a ƙasar nan.

Kwamandan rundunar sojin sashi na 8, Godwin Mutkut.
"Ku Mika Wuya Ko Mu Tura Ku Lahira" Rundunar Soji Ta Aike da Sako Ga Yan Bindiga Hoto: channelstv
Asali: UGC

Babban kwamandan rundunar sojin sashi na 8 a hukumar soji, Manjo Janar Godwin Mutkut ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a Gusau, babban birnin Zamfara.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika, An Kama Wani Mai Hannu a Kazamin Harin da Aka Kai Wa Babban Malami a Najeriya

Channels tv ta rahoto cewa jim kaɗa bayan kaddamar ofishin RMS a sansanin dakarun sojin Birged ta 1, kwamandan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu wanda ya tattauna da su gabanin su shiga jeji amma yanzu da suka ga luguden wuta na ɗai-ɗai ta su shi ne suke neman a tattauna, ni ba zan kira haka tattauna wa ba, su fito kawai su miƙa wuya."
"Batun tattauna wa wani makirci ne kawai kuma an jaraba a baya abun be daɗi ba, sabida haka don me za a sake maimaita wannan kurkuren?"

Kwamandan ya ƙara da cewa Sojoji ba zasu yi ƙasa a guiwa ba a ci gaba da ƙoƙarin kakkaɓe yan ta'adda daga shiyyar Arewa ta Yamma baki ɗaya.

Wane shiri Sojoji ke yi wa yan ta'adda?

Ya jaddada cewa rundunar soji ba zata tattauna da 'yan bindiga ba, maimakon haka zata farauce su har inda suke ɓuya ta tura su zuwa lahira.

Kara karanta wannan

Miji Da Mata Sun Yi Basajar Shiga Musulunci Yayin Da Suka Tafkawa Liman Sata a Yobe

Ya ce matuƙar 'yan bindiga suna son tsira daga hannun dakarun soji, zabi ɗaya gare su, su fito daga cikin inda suka ɓuya su miƙa wuya.

A cewarsa, duk da yanayin daminar da ake ciki, Sojoji sun ci gaba da shiga yankuna masu haɗari kamar Shinkafi, Zurmi, Tsafe, Ɗansadau a Zamfara suna ragargazan yan bindiga.

Gwamna Sani Ya Fara Yunkurin Dawo Da Zaman Lafiya Kaduna, Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro 3

A wani labarin kuma Gwamna Uba Sani ya gana da manyan hafsoshin tsaro 3 a shirinsa na haɗa hannu da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a Kaduna.

Uba ya sha alwashin cewa gwamnatinsa zata bai wa hukumomin tsaro haɗin kai da goyon baya a ƙoƙarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel