Titin Zuwa ‘Yan Kura Da Ke Birnin Kano Ya Cika Da Tarin Shara Da Ta Hana Masu Abin Hawa Bi Ta Kansa
- Sharar da ‘yan kasuwa ke zubarwa daga shagunansu ta yi sanadin cushe babban titin Court Road da ke Sabongari cikin birnin Kano
- Titin dai na daga cikin manyan hanyoyin da ake bi zuwa kasuwar ‘Yankura da ma wasu sassa na birnin
- Hukumar tsaftar muhalli ta jihar wato REMASAB, ta ce tana sane da lamarin, kuma za ta sanya mutanenta su kwashe sharar
Kano - Titin Court Road da ke cikin birnin Kano, ya cike da tarin shara wacce ta mamaye shi ta yadda masu ababen hawa basa iya bi ta kansa.
Titin wanda yake a yankin Sabongari, ya kasance daya daga cikin hanyoyin da a ke bi wajen shiga kasuwar Yankura dake cikin birnin na Dabo.
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da ke hada-hada a yankin, sun koka kan barazan kamuwa da cututtuka sakamakon sharar da aka jibge a kan titin. Sun bayyana hakan ne a zantawarsu da jaridar Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Yan kasuwar ne suka tara sharar da kansu
Bayanai na nuni da cewa ‘yan kasuwar ne da kansu suka tara sharar saboda takamar cewa gwamnatin jihar za ta sa a kwashe.
Daga cikin ayyukan da gwamnati mai ci a yanzu ta yi, akwai ma’aikatan kwashe shara da ta sanya aikin kwashe ilahirin sharar dake cikin birnin Kano.
A cikin kwanakinsu na farko, sun yi nasarar kwashe akalla tan 600 na sharar da aka tara a wurare daban-daban na birnin.
REMASAB za ta sa a kwashe ilahirin sharar
Gwamnati mai ci a kwanakinta na farko a kan mulki, ta kuma sanar da dawo da Hukumar Tsaftar Muhalli ta jihar Kano (REMASAB), hannun gwamnatin jiha.
Kafin zuwan gwamnatin Abba, hukumar ta REMASAB ta kasance ba a hannun gwamnatin jihar ba.
Daraktan REMASAB, Ahmadu Haruna Danzago ya bayyana cewa hukumar na sane da lamarin kuma za ta tura mutanenta domin kwashe sharar a ranar Juma’ar nan.
Abba Gida Gida ya ce ko kadan bai yi nadamar rusau da yake yi a Kano ba
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ko kadan babu nadama a ayyukan rusau da yake gudanarwa a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a hirarsa da rediyon Freedom.
Asali: Legit.ng