Masana: Amfanin Ayyana Dokar Ta Baci Kan Samar da Abinci Ga Yan Najeriya

Masana: Amfanin Ayyana Dokar Ta Baci Kan Samar da Abinci Ga Yan Najeriya

  • Masana sun bayyana yadda dokar ta ɓaci zata taka rawa wajen daidaita rayuwar 'yan Najeriya masu matsakaicin ƙarfi
  • Kabiru Adamu ya ce dokar ta ƙara bayyana alamun cewa shugaban ƙasa Tinubu yana sauraron koken talakawan Najeriya
  • Sai dai a nasa hangen, Johnson Chukwu, ya ce akwai buƙatar shugaba Tinubu ya fara magance matsalar da ta kawo ƙarancin abinci

Wasu masana biyu sun yi bayani kan ɓangarorin da 'yan Najeriya zasu amfana da matakin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na ayyana dokar ta ɓaci kan samar da abinci a Najeriya.

Shugaban Beacon Security Consulting Agency, Kabiru Adamu, ya ce ayyana dokar ta ɓaci kan batun samar da isasshen abinda alamu ne ƙarara da ke nuna Tinubu na sauraron koken talakawa.

Kabiru Adamu tare da Johnson Chukwu.
Masana: Amfanin Ayyana Dokar Ta Bace Kan Samar da Abinci Ga Yan Najeriya Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Haka nan wani masanin tattalin arziki, Johnson Chukwu, ya ce wannan doka na nufin shugaban ƙasa na da karfin ikon tsoma baki kan batun samar da abinci, rabawa da wadatarsa.

Kara karanta wannan

Shugaban Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Batun Samar da Abinci a Najeriya, Ya Bada Sabon Umarni

Masanan biyu sun yi wannan tsokaci ne a kafar Channels tv cikin shirinsu mai taken, "Politics Today" ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A nasa jawabin Adamu ya ce:

"Abu mai muhimmanci shi ne ɗan Najeriya mai matsakaicin ƙarfi zai samu damar ciyar da kansa da iyalansa, wanda hakan zai taimaka wajen toshe wa 'yan ta'adda ƙofar zuwa su yaudari wasu wawaye a cikin al'umma."

Adamu ya bayyana cewa wannan dokar ta jawo aikin samar da isasshen abinda ya matso kusa-kusa da harkokin shugabanci a Najeriya.

A cewarsa matukar aka yi tsari mai kyau na tsawon lokaci, to duk abinda ya shafi wadatar abinci cikin rahusa ta yadda masu matsakaicin ƙarfi zasu iya saye, zai dawo kan hanya.

Menene asalin abinda ya kawo ƙarancin abinci?

A nasa bangaren, Johnson Chukwu, ya ce a ganinsa babban abinda ya kamata a yi la'akari da shi shine tushen abinda ya kawo ƙarancin abinci a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1

Ya ƙara da cewa Najeriya ba ta shiga ibtila'in fari, rashin ƙasar noma ko rashin gonaki ba amma ƙalubalen shi ne ƙasar nan na fama da matsalar tsaro a shiyyoyin da ake noma.

Ya ce:

"Idan dagaske shugaban kasa yana son kawo karshen ƙarancin abinci, akwai buƙatar ya magance ta'addanci a Arewa maso Gabas, yan bindiga a Arewa maso yamma da rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya."

Mista Chukwu ya koka kan cewa tallafin da bankuna ke bayarwa a aikin gona ba ya kawo sauyin komai a ɓangaren noma da kiyo.

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Samar da Abinci a Najeriya

A ɗazu mun kawo muku cewa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta ɓaci game da batun aamar da isasshen abinci a Najeriya.

Ya kuma bada umarnin a gaggauta buɗe rumbun gwamnati, a fito takin zamani da hatsi a rabawa manoma da magidanta a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kujerar Shugaban APC Na Tangal-Tangal Bayan Wata 15, Zai San Makomarsa a NEC

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262