Malam Daurawa Ya Fara Shirin Daura Auren Mutum 1,000 a Jihar Kano
- Shugaban hukumar Hisbah da gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a Kano ya shiga Ofis ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, 2023
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce tuni suka fara shirye-shiryen ɗaura aure 1,000 a faɗin kananan hukumomi 44
- Ya ce hukumar Hisbah ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta tsaftace Kano daga kowane irin aikin rashin ɗa'a
Kano state - Sabon Kwamandan rundunar 'yan sandan Musulunci watau Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daura, ya kama aiki gadan-gaban.
Sheikh Daurawa ya ce tuni shirye-shirye suka yi nisa na aurar da 'yan mata da zawarawa 1,000 karkashin rundunar Hisbah a faɗin jihar Kano.
Kwamandan ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan shiga Ofis wanda ya ɗora a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.
Idan baku manta ba Daurawa ya yi aiki a matsayin kwamandan Hisbah a lokacin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Ganduje.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan Daurawa ya bar muƙamin a shekarun baya, a halin yanzu gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake dawo da Shehin Malamin, ya naɗa shi kwamandan Hisbah a karo na uku.
Zamu raba Fam kowace karamar hukuma - Daurawa
Da yake jawabi jim kaɗan bayan shiga Ofis, Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana cewa sabon gwamna, Abba Gida-Gida dagaske yake wajen inganta walwalar mutanen Kano.
Game da ƙulla aure 1,000 kuwa, Daurawa ya ce sun kafa kwamitoci daban-daban domin tabbatar da an samu nasarar haɗa ɗaruruwan ma'aurata a faɗin jihar Kano.
Ya kuma kara da cewa hukumar Hisbah zata raba Fom guda 20 ga kowace ƙaramar hukumar a cikin ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.
Ya ce:
"Zamu ba kowane kwamandan ƙaramar hukuma Fam 20, ya tantance mutanen da suka cike domin ɗaura musu aure."
Wace hanya za a samu kuɗin aikata wannan kyakkyawan aiki?
Sheikh Daurawa ya yi bayanin cewa kofar hukumar Hisbah a buɗe take ga duk wanda ke da niyyar tallafawa wajen ganin an cimma nasarar ɗaura aure 1000.
"Hukumar Hisbah ta ba zata yi ƙasa a guiwa ba a kokarinta na tsaftace jihar Kano daga aikata munanan ɗabi'u," inji Malam Daurawa.
Gwamnan Jigawa Umar Namadi Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 16
A wani labarin kuma Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya rantsar da sabbin kwamishinoni 16 a gidan gwamnatinsa da ke Dutse.
Gwamna Namadi ya buƙaci kwamoshinoni su yi aiki bisa tsoron Allah, gaskiya da riƙon amanar al'umma da kuma sauke haƙƙi.
Asali: Legit.ng