Yanzu Yanzu: Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Ciyo Bashin N500bn Don Ragewa Yan Najeriya Radadi
- Majalisar wakilai ta yi na'am da bukatar Shugaban kasa Bola Tinubu da ciyo bashin naira biliyan 500
- Za a yi amfani da kudin ne wajen siyawa yan Najeriya kayan tallafi domin rage masu radadin cire tallafin man fetur
- Majalisar ta amince da bukatar ne a zamanta na ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli
Abuja - Majalisar wakilai ta amince da bukatar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na neman yin gyara a kan kasafin kudin shekarar 2022, jaridar Punch ta rahoto.
Majalisar ta amince da hakan ne bayan bukatar da Tinubu ya gabatar na daukar naira biliyan 500 domin tallafawa yan Najeriya da nufin rage masu radadin janye tallafin man Fetur.
Bukatar ta tsallake karatu na farko, na biyu da na uku a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.
Kuma Dai: Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Amince Masa Ciyo Bashin Dala Miliyan 800 Daga Bankin Duniya, Ya Sanar Da Abin Da Zai Yi Da Kudin
Majalisar ta amince da bukatar Shugaban kasa Tinubu na ciyo bashin naira biliyan 500
Sai dai kuma, majalisar ta amince da bukatar shugaban kasar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli bayan mambobin majalisar sun bayar da gudunmawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun farko mun ji cewa Tinubu ya bayyana cewa biliyan 500 kawai yake son ciyowa bashi daga cikin karin sama da biliyan 800 da aka yi a kasafin kudin shekarar 2022.
Tinubu ya ce yan Najeriya miliyan 12 za su dunga samun N8,000 duk wata
A wani labarin kuma, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa talakawa mutum miliya 12 za su riƙa samun N8,000 kowane wata har na tsawon wata shida domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
A cikin wata takarda da ya like zuwa ga majalisar wakilan wacce kakakinta Abbas Tajudeen ya karanto a zaman majalisar na ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, Tinubu ya ce za a biya kudin ne domin rage radadin da talakawa ke ciki.
Har ila yau, Shugaban kasar ya ce biyan kudin zai Sa Yan Najeriya miliyan 60 su ci gajiyar wannan shiri. Ya kuma bayyana cewa za a dunga tura kudin ne kai tsaye zuwa asusun wadanda za su ci gajiyar shirin don gudun kada ya shiga hannun wadanda za su hamdame da yin babakere a Kansu.
Asali: Legit.ng