Gwamnatin Kebbi Ta Kubutar da Mutane 30 Daga Hannun 'Yan Bindiga

Gwamnatin Kebbi Ta Kubutar da Mutane 30 Daga Hannun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta ceto mutum 30 da suka fito daga jihohi 3 daga hannun 'yan bindiga
  • Shugaban ƙaramar hukumar Danko-Wasagu, Honorabul Aliyu Bena, ya yaba wa gwamna Nasir Idris bisa wannan nasara
  • Ya ce a halin yanzun an kai mutanen babban Asibiti domin duba lafiyarsu gabannin sake haɗa su da iyalansu

Kebbi state - Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin gwamna Nasir Idris, ta sa baki an kuɓutar da mutane 30 daga hannun miyagun 'yan bindigan jeji.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa 'yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen a ƙaramar hukumar Danko Wasagu da ke cikin jihar Kebbi, Arewa maso yamma.

Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris.
Gwamnatin Kebbi Ta Kubutar da Mutane 30 Daga Hannun 'Yan Bindiga Hoto: Kebbi Social Media Forum
Asali: Facebook

Shugaban ƙaramar hukumar Danko-Wasagu, Honorabul Hussaini Aliyu Bena, shi ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a Birnin Kebbi ranar Laraba, 12 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Shirya Karban Gwamnonin PDP 5 Da Zaran Sun Shirya Sauya Sheƙa Zuwa Cikinta

Aliyu Bena ya nuna matuƙar farin cikinsa bisa wannan nasara ta ceto mutanen ƙaramar hukumar da yake jagoranta daga hannun miyagun 'yan bindiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ya zama wajibi mutanen Danko-Wasagu su yaba wa gwamnatin Kebbi karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris na jam'iyyar APC.

Ya kuma ƙara da bayanin cewa mutanen da suka shaƙi iskar 'yanci sun fito daga garin Kontagora, jihar Neja, Damari, Kabba da Kajiji a jihohin Sakkwato da Zamfara yayin da wasu kuma suka fito daga Bena, jihar Kebbi.

Ta ya gwamnati ta ceto mutanen?

Da yake karin bayani kan yadda aka ceto mutanen, Ciyaman ɗin Danko-Wasagu ya yaba wa kwamandan rundunar soji mai kula da jihohin Sakkwato, Zamfara da Kebbi.

Ya ce kwamandan ya cancanci yabo bisa haɗa tawagar gwarazan jami'an tsaro, waɗanda suka samu nasarar ceto mutanen daga hannun tsagerun 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Masu Sana'ar Jari Bola a Borno

A cewarsa, tuni aka garzaya da waɗanda lamarin ya shafa babban Asibiti domin bincikar lafiyarsu kafin maida su cikin iyalansu, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Gwamna Sani Ya Fara Yunkurin Dawo da Zaman Lafiya, Ya Gana da Hafsoshin Tsaro 3

A wani rahoton Gwamna Uba Sani ya gana da manyan hafsoshin tsaro 3 a shirinsa na haɗa hannu da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a Kaduna.

Da yake ƙarin haske kan ganawarsa da hafsoshin tsaron a lokuta daban-daban, Gwamna Uba Sani ya ce sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262