Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa

  • A ranar Alhamis 13 ga watan Yulin 2023, majalisar dattawan Najeriya ta shiga tantance manyan sabbin hafsoshin tsaro
  • Manyan hafsoshin tsaron na ƙasa sun bayyana ne a gaban majalisar domin a tantance su biyo bayan naɗin da Shugaba Tinubu ya yi musu
  • Tun da farko Shugaba Bola Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa ga majalisar dattawan ta Najeriya domin neman ta amince da naɗin da ya yi na hafsoshin tsaron

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta fara tantance manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan waɗanɗa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Majalisar dattawan za ta tantance babban hafsan tsaro na ƙasa (CDS), Manjo Janar Christopher Musa, Manjo T. A Lagbaja, shugaban hukumar sojin ƙasa a Najeriya (COAS), Rear Admiral E. A Ogalla, shugaban hukumar sojojin ruwa ta ƙasa da AVM H.B Abubakar, shugaban hukumar sojin saman Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa

Majalisar dattawa ta fara tantance manyan hafsoshin tsaro
Manyan hafsoshin tsaro yayin shiga zauren majalisa Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

Sauran sun haɗa da DIG Kayode Egbetokun, muƙaddashin sufeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP) da Manjo Janar EPA Undiandeye, shugaban hukumar tattara bayanan fasaha ta ƙasa.

Shugaba Tinubu ya buƙaci majalisar ta amince da naɗin da ya yi musu

Shugaban ƙasa Bola Tinubu a wata wasiƙa da ya aikewa da majalisar dattawan ranar Litinin, ya buƙaci da ta tabbatar da naɗin hafsoshin tsaron, rahoton Channels tv ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Domin fara tantance su, manyan hafsoshin tsaron sun iso harabar majalisar dattawan ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe domin bayyana a gaban ƴan majalisun da aka shirya zai gudana da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

A zaman majalisar na ranar Alhamis, majalisar dattawan ta fara tantance manyan hafsoshin tsaron, inda kowannensu ya gurfana a gabanta ya yi bayanin yadda za su daƙile matsalar tsaron ƙasar nan idan aka tabbatar da naɗin da aka yi musu.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga Masu Yawa a Jihar Arewa, Sun Kwato Muggan Makamai

Majalisar dai ta ba kowanne daga cikinsu mintuna biyu domin gabatar da kansa knda daga bisani ta fara tantancesu a ƙebe da misalin ƙarfe 12:42 na rana.

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabbin Hafsoshin Tsaro

A baya rahoto ya zo cewa, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron ƙasa da muƙaddashin Sufeta Janar na ƴan sanda.

Shugaban ƙasar ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ne bayan ya sallami magabatansu daga aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng