Budurwa Ta Shiga Damuwa Yayin da Saurayinta Ya Tura Mata N500k Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amanarta

Budurwa Ta Shiga Damuwa Yayin da Saurayinta Ya Tura Mata N500k Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amanarta

  • Wata matashiya yar Najeriya ta shiga rudani kan ko ta yafewa saurayinta ko kada ta yafe mai bayan ya aika mata N500k na ban hakuri
  • Ta kai masa ziyarar bazata amma ta tafi da bacin rai bayan ta kama shi yana cin amanarta da wata
  • Kafin ta kai ga toshe lambar wayarsa, sai ya aika mata rabin miliyan a asusun bankinta amma ya dau mata alkawari

Wata budurwa yar Najeriya mai suna Precious ta shiga cikin rudani bayan saurayinta ya aike mata da rabin miliyan saboda ta kama shi yana cin amanarta.

Precious ta bayyana a Twitter cewa ta kai masa ziyarar bazata sakamakon dawowa da ya yi daga tafiya sannan ta shiga gidan nasa da sifiyar makuli.

Saurayi ya turawa budurwarsa N500k bayan ta kama shi yana ci mata amana
Budurwa Ta Shiga Damuwa Yayin da Saurayinta Ya Tura Mata N500k Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amanarta Hoto: RealPeoplePhoto, Lona Studio, Bloomberg
Asali: Getty Images

Ga mamakinta, Precious ta gano cewa yana cin amanarta sannan ta fita ta bar gidan cikin hawaye.

Kara karanta wannan

"Kana Bin Sa’ar Uwarka”: Uba Ya Kama Dansa Mai Shekaru 21 a Gidan Hajiyar Birni, Bidiyon Ya Yadu

Precious ta ce ta ci kuka har idanunta sun yi bulu-bulu sannan ta yi niyar toshe layin wayarsa a lokacin da ta isa gida lokacin da wani sako ya shigo mata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Saurayin Precious ya fanshi laifin da ya yi mata

Sakon daga saurayin nata ne. Ya ce ya aika mata da kudi N500k don ban hakuri sannan ya yi alkawarin cewa zai gyara.

"Don takaita dogon labarin na isa gida sannan ina shirin toshe lambarsa lokacin da na ga "babi ina mai baki hakuri sosai duba wayarki yanzun nan na aika maki 500k ki karba saboda dukkan hawayen da kika rasa da daddaren nan, na yi alkawarin gyarawa," Precious ta rubuta.

Matashiyar ta ce nan take sakon ya warkar da radadin da take ji a zuciyarta sannan ta shiga rudani kan ko ta yakewa masoyin nata ko kada ta yafe.

Kara karanta wannan

“Dukana Take Yi”: Miji Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha a Hannunta

Kalli wallafarta a kasa:

Mutane sun bayyana ra'ayinsu

@omotolani_Adeyi ta ce:

"Ya siya yafiyarki a yau, yawan kudin da ya baki ba shine sigar labarinba, zai sake siyar yafiyarki wata rana domin ya san kudin ne ainahin abun da kike so. Abu guda da ya kamata ki sani shine ya dade da budurwar da kika kama shi da ita."

@kabughoesther5:

"Kawai ki sa ya rubanya kudin sannan ki yafe masa. Idan kika sake kama shi, ya ninka kudin sau uku kuma sai a ci gaba da rayuwa."

@abbey_aluko:

"Akalla dai kin cika kudirinki na bashi mamki sannan kema kin sha mamaki...Lamari mai cike da nasara nasara."

@cherrychila57:

"Wato yanzu dai kin zubar da miyan koda yake kada ki rabu da shi, ki ci gaba da zuwa gidansa ba tare da ya gayyace ki ba don baba ya ci gaba da tura maki 500k."

Bidiyon matashi tare da wata yarinya a otal ya ta da kura

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

A wani labarin, mun ji cewa wani bidiyon matashi dan Najeriya yana shiga otal da yar karamar budurwa ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya.

Wani mai amfani da TikTok, wanda ya wallafa bidiyon, ya nemi Allah ya kare kananan yara masu tasowa, cewa Allah ne kadai zai iya cetonmu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng