Kotu Ta Daure Matashin Fasto Shekaru 2 A Gidan Kaso Bayan Fasa Shagon Wani, Ya Fadi Dalilin Yin Satar

Kotu Ta Daure Matashin Fasto Shekaru 2 A Gidan Kaso Bayan Fasa Shagon Wani, Ya Fadi Dalilin Yin Satar

  • Kotu ta daure wani Fasto da ake zargi da fasa shago da kuma yin satar sinadarai a jihar Ondo
  • Wanda ake zargin, Friday Okeneji mai shekaru 29 ya ce ya aikata hakan ne don rashin aikin yi
  • Okeneji shi ne shugaban majami'ar Iwaro Oka Akoko, ya aikata laifin a ranar 2 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Kotun majistare da ke Akure a jihar Ondo ta daure matashin Fasto shekaru biyu a gidan gyaran hali bisa zargin sata.

Faston Friday Okeneji mai shekaru 29 ana zargin shi da fasa shago da satar sinadarai da suka kai kimanin N130,000.

Kotu Ta Daure Matashin Fasto Shekaru 2 A Gidan Kaso Bayan Satar Sinadari
Kotun Majistare Ta Daure Fasto Shekaru 2 A Gidan Kaso Bisa Zargin Satar Sinadari Da Ya Kai N130,000. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Okeneji wanda shi ne shugaban majami'ar Iwaro Oka Akoko da ke jihar Ondo ya aikata laifin a ranar 2 ga watan Yuli, Vanguard ta tattaro.

Wanda ake zargin ya amince da dukkan laifukansa

Kara karanta wannan

Kaico: Akan Biredi, Wasu Sun Kashe Matashi Mai Jini a Jika, Sun Gamu da Fushin 'Yan Sanda

Wanda ake zargin ya amince da dukkan tuhume-tuhumen da ake a kansa inda ya ce ya aikata hakan ne don ba shi da abin yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya fadawa kotu cewar ba shi da wata hanyar samun kudi shiyasa ya aikata hakan, cewar Tribune.

Ya kara da cewa mahaifiyarsa ce ta mutu kuma dole shi zai nemo kudin bikin binne ta wanda ya kai N150,000 shi kuma ba shi da aikin da zai nemo wadannan kudade.

Faston ya fadi dalilin yin satar a gaban kotu

Ya ce:

"Dole sai na nemo kudin binne mahaifiya ta har N150,000 a watan Agusta mai zuwa kuma bani da hanyar samun kudi.

Mai shari'a Damilola Sekoni ta ce ana zargin Okeneji da laifuka biyu tare da daure shi na shekaru biyu a gidan kaso da biyan tara N100,000.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Jero Irin Mutanen da Shugaban Kasa Zai Dauko Su Zama Ministoci

Ta bukaci wanda ake zargin da ya yi koyi da koyarwar addinin Kirista tare da zama mai kwazo da addu'a, Daily Trust ta tattaro.

'Yan Sanda Sun Kama Ma'aikatan Jinya 2 Da Mai Gadi Kan Zargin Satar Mahaifa

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ondo sun cafke wasu ma'aikatan jinya biyu kan zargin satar mahaifa.

Ma'aikatan jinyan na aiki ne a cibiyar lafiya ta Comprehensive da ke Owo cikin jihar.

Daga cikin wadanda aka kaman akwai mai gadin asibitin wanda ya hada baki da sauran ma'aikatan don aikata laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.