Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga Uku a Jihar Plateau

Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga Uku a Jihar Plateau

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka miyagun ƴan bindiga a jihar Plateau a wata arangama da suka yi
  • Dakarun sojojin sun halaka ƴan bindigan ne a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar mai fama da rikicin ƴan bindiga
  • Kwamandan atisayen 'Operation Safe Haven' ya sha alwashin ci gaba da kakkaɓe ƴan bindigan da suka addabi jihar

Jihar Plateau - Dakarun sojojin Najeriya na atisayen 'Operation Safe Haven' sun halaka ƴan bindiga uku a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Jaridar The Cable ta tattaro cewa dakarun sojojin sun yi musanyar wuta ne da ƴan bindigan bayan sun yi musu kwanton ɓauna akan titin hanyar Mangu/Pushit a ranar Laraba.

Dakarun sojoji sun sheke 'yan bindiga uku a jihar Plateau
Dakarun sojojin Najeriya Hoto: Thecableng.com
Asali: UGC

A lokacin fafatawar wacce ta yi sanadiyyar halaka ƴan bindiga uku, sojojin sun kuma ƙwato bindiga uku ƙirar AK47, miyagun makamai, babur guda ɗaya da katin aiki na wani kurtun ɗan sanda, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1

Majiyoyi daga cikin dakarun sojojin sun bayyana cewa sauran ƴan bindigan sun arce daga fafatawar ɗauke da harbin bindiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Halaka ƴan bindigan dai na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su murƙushe masu tayar da ƙayar baya a jihar ta Plateau.

Dakatun sojojin za su ci gaba da fatattakar ƴan bindiga

Da yake magana kan lamarin, kwamandan atisayen, Abdusalam Abubakar, ya bayyana cewa dakarun sojojin za su ci gaba da gudanar da aikinsu bisa yadda tsarin doka ya tanada.

Abubakar ya ce dakarun sojojin za su ci gaba da nuna ba sani ba sabo wajen tabbatar da fatattakar ƴan bindigan da suka addabi jihar.

Ya bayyana cewa dakarun sojojin za su amsa kowane kiran gaggawa cikin cikin lokaci domin za a tura su zuwa ƙauyukan dake cikin ƙaramar hukumar ta Mangu mai fama da rikici.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Da Wasu Mutum Uku Sun Fada Komar 'Yan Bindiga, Sun Yi Awon Gaba Da Su

Dan Majalisa Ya Bukaci Al'ummar Plateau Su Kare Kansu

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Plateau, ya buƙaci al'ummar jihar da su tashi tsaye su kare kansu daga hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa a jihar.

Dachung Musa Bagos ya buƙaci al'ummar jihar da su bi hanyoyin da tsarin mulki ya tanadar su kare kansu tun da gwamnati ta gaza

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng