Cire Tallafi: ’Yan Majalisa Sun Fadi Yadda Suke Cin Bashi Kafin Wata Ta Kare, Sun Bukaci Karin Albashi

Cire Tallafi: ’Yan Majalisa Sun Fadi Yadda Suke Cin Bashi Kafin Wata Ta Kare, Sun Bukaci Karin Albashi

  • Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da wahalhalu bayan cire tallafi, ‘yan majalisar Wakilai suma sun koka kan yanayin da suke
  • Mambobin sun bukaci gwamnatin Tarayya ta kara musu albashi da alawus saboda mawuyacin halin da da suma suke ciki
  • Sun bayyana yadda suke cin bashi saboda albashin ba ya isarsu yayin da kakakin majalisar ya ce bukatar ba ta kasafin kudi na 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Mambobin majalisar Wakilai a Najeriya sun bukaci karin albashi da alawus saboda cire tallafin man fetur a kasar.

‘Yan majalisar sun ce su ma fa suna cikin wani yanayi saboda yadda tattalin arzikin kasar ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Yan Majalisa Sun Fadi Yadda Suke Cin Bashi Kafin Wata Ta Kare Bayan Cire Tallafi Sun Nemi Karin Albashi
Yan Majalisa Sun Bayyana Halin Da Suka Shiga Tun Bayan Cire Tallafi A Kasar. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Wannan bukata na zuwa ne bayan mambobin sun fito daga wata ganawa ta musamman a ranar 11 ga watan Yuli bayan zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Na San Yan Najeriya Na Shan Bakar Wahala Amma A Kara Hakuri, Tinubu Ya Fadi Tanadin Da Ya Yiwa Talakawansa

'Yan majalisar sun bayyana halin da suke ciki bayan cire tallafi

Korafe-korafen mambobin a cikin majalisar kan karin albashin ya fara tada kura wanda yakan yasa dole suka shiga ganawa ta gaggawa da shugabannin majalisar kadai don dakile matsalar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan majalsar har ila yau, sun bukaci shugaban majalisar, Tajudden Abbas ya musu bayanin rashin biyansu albashi a kan lokaci wanda hakan yasa suka nemi bashi.

Daya daga cikin mambobin majalisar daya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa albashinsu baya iya wadatar dasu a wata don haka suke bukatar kari.

Ya ce:

“Babu wanda ya yi magana a kan kudi ko ana biyan mu ko a’a.”

Premium Times ta tattaro cewa mambobin sun bukaci karin albashin ne saboda yadda rayuwa ta yi tsada a kasar bayan cire tallafin man fetur wanda ya haddasa hauhawan farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

Sun bukaci karin albashi don rage radadi

Mamban ya ce kakakin majalisar bai musu alkawarin komai a kan karin albashin ba soboda wannar bukata dole sai an saka ta a cikin kasafin kudi wanda akwai tsari a ciki.

Ya kara da cewa kakakin ya fada musu cewa bukatar tasu ba ta cikin kasafin kudi na 2023, don haka babu wani alkawari da ya yi, The Whistler NG ta tattaro.

Ya kara da cewa:

“Dukkanmu munsan halin da ake ciki a kasar nan, muna fama da matsaloli sosai a kasar saboda cire tallafin man fetur.”

Tinubu, Shettima Da Sauran Yan Siyasa Za Su Samu Karin Albashi Da Kashi 114

A wani labarin, Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran 'yan siyasa sun samu karin albashi da kashi 114.

Hukumar Kula da Rarraben Kudaden Shiga (RMAFC) ta amince da karin fiye da kashi 100 ga zababbun 'yan siyasa.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Sahale Masa Ciyo Bashin Naira Biliyan 500, Ya Bayyana Dalili

Sauran wadanda wannan karin zai shafa akwai gwamnoni da 'yan majalisun Tarayya da ma'aikatan shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.