Gwamnan Neja Ya Yi Watsi Da Batun Tallafin Karatu, Ya Ce Zai Rage Ingancin Ilimi a Jihar

Gwamnan Neja Ya Yi Watsi Da Batun Tallafin Karatu, Ya Ce Zai Rage Ingancin Ilimi a Jihar

  • Gwamnatin jihar Neja ta ce ba za ta riƙa bayar da tallafin karatu ga ɗaliban jihar ba
  • Gwamnan jihar, Umaru Mohammed Bago ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da shugabannin jami'ar New Gate
  • Bago ya ce gwamnatinsa za ta samar da wani tsari na musamman ga ɗaliban da ke karatu a ɓangaren likitanci

Minna, Neja - Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago ya yi watsi da batun bayar da tallafin karatu ga dalibai a jihar.

Ya ce ci gaba da ba da tallafin karatu zai iya shafar ingancin ilimin da ake bayarwa a makarantun jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Umar Bago ya yi watsi da ba da tallafin karatu a jihar Neja
Gwamnan Neja Umar Bago ya ce ba da tallafin karatu zai rage ingancin ilimi a jihar. Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Bago ya nemi a riƙa gabatar da ƙananun kwasa-kwasai a manyan makarantun jihar

Umar Bago ya jaddada buƙatarsa ta ganin manyan makarantu sun samar da tsarukan gudanar da ƙananun kwasa-kwasai masu muhimmanci ga waɗanda ba su samu damar yin karatun digiri ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Yi Tonon Silili, Ya Bayyana Ainihin Masu Kashe Al'umma a Jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yi bayanin ne a lokacin da mahukunta da ma’aikatan jami’ar New Gate suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Minna.

Duk da haka, Umaru Bago ya bayyana cewa ya kamata a gano ɗalibai masu hazaƙa domin ɗaukar nauyin karatunsu a matsayin ƙarfafawa.

Gwamnan ya nuna rashin jin ɗaɗinsa kan ƙarancin likitoci a jihar

Gwamna Bago ya kuma nuna rashin jin ɗaɗinsa kan rashin isassun likitoci a jihar, inda ya ce gwamnati ta ƙudiri aniyar ƙarfafa gwiwar masu son yin karatu a fannin kiwon lafiya.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta cike wannan wawukeken giɓin ta hanyar tallafawa duk waɗanda ke son karantar fannin likitanci da makamantansa.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta samar da tsarin bai wa ɗaliban likitancin kaso 50% na kuɗin karatun nasu, da zummar za su yi wa jihar aiki na wani ɗan lokaci a yayin da suka kammala karatunsu.

Kara karanta wannan

"Ku Cire Tsoro" Gwamnan Arewa Ya Yi Karin Haske Kan Matakai 2 da Zai Ɗauka Kan Malamai 7,000 A Jiharsa

Sai dai a cikin wasu kwanakin da suka shuɗe, jaridar Vanguard ta yi rahoto kan cewa gwamnatin Neja ta yi alƙawarin samar da motocin da za su riƙa kai ɗaliban makarantun firamaren gwamnati makaranta kyauta.

A cewar gwamnan, sun ɗauki wannan matakin ne domin ragewa mutanen jihar raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki.

Gwamnan jihar Neja ya shawarci al'ummar jihar su taƙaita zirga-zirgar da suke yawan yi

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto inda gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya shawarci al'ummar yankin Kagara su taƙaita yawan zirga-zirgar da suke yi saboda dalilai na tsaro.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai wa sarkin Kagara, Malam Ahmed Garba Gunna ziyarar barka da sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng