Matashi Dan Shekara 21 Ya Bar Makaranta Don Bin Hajiyar Birni, Mahaifinsa Ya Kama Shi a Gidanta

Matashi Dan Shekara 21 Ya Bar Makaranta Don Bin Hajiyar Birni, Mahaifinsa Ya Kama Shi a Gidanta

  • Wani uba ya fusata sosai bayan ya gano cewa dansa mai shekara 21 yana da wata hajiyar birni wacce yake zama da ita
  • A wani bidiyo da ya yadu a Twitter, ya gano inda dan nasa yake a gidan hajiyar birnin sannan ya hada yar dirama
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani sosai ga bidiyon inda da dama suka caccaki matashi a kan neman wacce ta isa haifansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyo da ya yadu ya nuno wani matashi dan Najeriya mai shekara 20 wanda ya bar makaranta domin tarewa da wata hajiyar birni mai kudi.

A bidiyon, mahaifin yaron ya nuna rashin jin dadinsa game da halin yaron nasa, yana mai cewa ya so dansa ya je makaranta amma maimakon haka, ya zabi bin wacce ta isa ta haife shi.

Kara karanta wannan

“Dukana Take Yi”: Miji Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha a Hannunta

Uba ya kama dansa a gidan Hajiyar birni
Matashi Dan Shekara 21 Ya Bar Makaranta Don Bin Hajiyar Birni, Mahaifinsa Ya Kama Shi a Gidanta Hoto: @abd_lar_thev/Twitter.
Asali: Twitter

Hajiyar birnin ta isa wajen sannan ta janye yaron daga hannun mahaifinsa, tana mai cewa shekaru ba komai bane kawai adadi ne.

A lokacin da mahaifin nasa ya tunatar da yaron cewa shi kadai ke gareshi, matar ta dakatar da shi cewa yaron na ita a rayuwarsa sannan cewa za su samar da iyalinsu tare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A nasa bangaren, yaron ya nuna rashin tarbiya ga mahaifin nasa yayin da ya ce ya rigada ya yanke shawarar kasance da hajiyar birnin duk da barazanar da mahaifinsa ya yi na sako yan sanda a lamarin.

Ya ci gaba da cewar 'makaranta duk bige ce' sannan ya yi watsi da shawarar komawa makaranta. Da take kare kanta, matar ta bayyana cewa yaron ya san ciwon kansa domin ya wuce shekaru 18.

"Rayuwata ce, ku bar ni na yi rayuwata," inji yaron.

Kara karanta wannan

“Zan Dauki Nauyin Mmesoma Ejikeme”: Miloniya Zai Tura Yarinyar Da Ta Kirkiri Sakamakon JAMB Dinta Waje Karatu

Jama'a sun yi martani

@cjxyz ya ce:

"Anyi mai asiri ne."

@D_KryptonianX ya yi martani:

"Wato ba za su iya shirya samari a gefen nan su yi masa mugun duka da zai gyara masa kwakwalwa ba...na rantse da Allah, kuna bata mun rai. Da Gayen ya sha mari da yawa..."

@OkomisoJoe ya ce:

"Zance cewa makaranta buge ce yana bata mun rai a duk lokacin da na ji matashi ya fadi haka."

Hoton Rahama Sadau da wani matashi farin fata ya ta da kura

A wani labari na daban, jama'a sun yi caaa a kan jarumar Kannywood, Rahama Sadau bayan bayyanar wani hotonta a soshiyal midiya.

An dai gano Rahama da wani matashin saurayi farin fata inda ta daura hannunta a kan kafadarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng