Tsawa Ta Yi Ajalin Masu Garkuwa Da Mutane 3 A Jihar Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Tsawa Ta Yi Ajalin Masu Garkuwa Da Mutane 3 A Jihar Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

  • Tsawa ta hallaka wasu da ake zargin masu garkuwa ne yayin da suke tsaka da aiki a yankin Oro da ke jihar Kwara
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa mutanen uku na daga cikin takwas da suka addabi yankin da hare-hare
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce suna kan bincike don gano ainihin abin da ya faru

Jihar Kwara - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun gamu da ajalinsu yayin da tsawa ta yi kaca-kaca da su a jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 10 ga watan Yuli a kauyen Oro Ago da ke karamar hukumar Ifelodun da ke jihar.

Murna Yayin Da Tsawa Ta Yi Ajalin Masu Garkuwa Da Mutane 3 A Arewacin Najeriya
Mutane Na Murna Bayan Tsawa Ta Yi Ajalin Masu Garkuwa Da Mutane 3 A Jihar Kwara. Hoto: The Discover Nigeria.
Asali: Facebook

Ana zargin wadanda suka mutun na cikin masu garkuwa takwas da suka addabi mazauna yankin.

Kara karanta wannan

"Idan Kika Yi Gaggawa, Za Ki Ga Gaggawa": Jarumar Fim Ta Magantu a Kan Mutuwar Aurenta 2, Ta Shawarci Yan Mata a Bidiyo

Masu garkuwan uku na daga cikin wadanda suka addabi yankin

Har ila yau, ana zargin suna daga cikin wadanda suka kai hari kauyen Iwo a cikin karamar hukumar Isin makwanni biyu da suka wuce.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani faifan bidiyo da ya ke yawo a kafar sada zumunta, an gano gwarwakin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutanen ne a kone, Daily Trust ta tattaro.

Mutanen uku sun kone kurmus sai wari suke, ba a iya gane su saboda tsananin kunan da suka sha, cewar Aminiya.

Yadda tsawa ta yi ajalin masu garkuwan

Alamu sun nuna cewa 'yan sa kai ne suka dauki faifan bidiyon inda aka jiwo muryar wani daga cikin bijilan din yana magana a kan gawarwakin.

Ya ce:

"Kokarin da muke na yaki da wadannan miyagu ya fara samun nasara, mu ne 'yan kwamitin sa kai wato bijilan na wannan yanki na Igbomina."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Sabuwar Cutar Mashako Da Ta Bulla a Jihar Yobe Ta Kashe Yara 30 Da Kwantar Da 42 a Asibiti

Muryar ta kara da cewa:

"Duk masu neman mu da sharri Allah zai wargaza lamarinsu, wadannan gawarwakin masu garkuwa ne da mutane da tsawa ta kashe su."

Daga cikin wadanda suka kai harin, ana zargin har da wadannan da tsawa ya kashe, cewar Leadership.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce bincike ne zai tabbatar da asalin abin da ya kashe su.

Amarya Da 'Yan Uwan Mijinta Sun Kubuta Daga Masu Garkuwa Da Mutane A Kwara

A wani labarin, wata amarya da 'yan uwan mijinta sun shaki iskar 'yanci bayan shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane.

An sako amaryar ce mai suna Rukayyat Musa da kannen mijinta biyu bayan sun biya kudin fansa na N7m.

Tun farko masu garkuwan sun bukaci sai sun biya N50m kafin a sako su a matsayin kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.