Gwamna Sani Ya Fara Yunkurin Dawo Da Zaman Lafiya Kaduna, Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro 3
- Gwamna Uba Sani ya gana da manyan hafsoshin tsaro 3 a shirinsa na haɗa hannu da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a Kaduna
- Ya ce sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi barazanar tsaro a jihar Kaduna da sauran jihohin maƙota
- A cewar hafsoshin tsaron, sun shirya kawo karshen yan bindiga, masu garkuwa da sauran masu aikata manyan laifuka a ƙasar nan
Kaduna state - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya fara yunƙurin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Uba Sani ya gana da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan uku a shirinsa na yauƙaƙa alaka da hukumomin tsaro domin kawo karshe taɓarɓarewar tsaro a Kaduna.
Gwamna Sani ya gana da babban hafsan tsaron ƙasa (CDS), Manjo Janar Christopher Musa, shugaban sojin ƙasa (COAS), Taoreed Lagbaja, da shugaban sojin sama, Air Vice Marshal Hassan Abubakar.
Muhimman batutuwan da suka tattauna
Da yake ƙarin haske kan ganawarsa da hafsoshin tsaron a lokuta daban-daban, Gwamna Uba Sani ya ce sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro a Kaduna da jihohin makota.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Malam Uba Sani ya ce:
"Duk da an samu nasarori da dama a yaƙi da matsalar tsaron jihar Kaduna, na sake tuna wa hafsoshin tsaron cewa akwai buƙatar ɗora wa kan nasarar da aka samu."
Uba ya sha alwashin cewa gwamnatinsa zata bai wa hukumomin tsaro haɗin kai da goyon baya a ƙoƙarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Haka zalika ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa sakon taya murna ga sabbin shugabannin tsaro a madadin mutanen jihar Kaduna baki ɗaya.
Zamu haɗa hannu da gwamnatin Kaduna
A nasu ɓangaren, manyan hafsoshin tsaron sun tabbatar wa gwamna Uba Sani cewa a shirye su ke su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Kaduna domin dawo da zaman lafiya.
A cewarsu, sun shirya kawo karshen ayyukan 'yan bindiga, masu garkuwa da sauran manyan ayyukan ta'addanci da nufin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gwamnatin Katsina Ta Kwantar da Hankalin Malaman S-Power, Ta Fadi Mataki Na Gaba
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Dikko Radɗa ta yi bayani domin yaye tsoron da ya mamaye zuƙatan malaman makaranta na shirin S-Power a Katsina.
Da yake jawabi ga ƙungiyoyin malaman S-Power guda biyu, na Sakandire da Firamare, Sakataren gwamnatin ya faɗa musu karsu ji tsoro ko su karaya da jarabawar gwajin da za'a musu.
Asali: Legit.ng