'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Mutane 3 Kan Kashe Matashi Bisa Zargin Satar Biredi, Hukumar Ta Yi Gargadi

'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Mutane 3 Kan Kashe Matashi Bisa Zargin Satar Biredi, Hukumar Ta Yi Gargadi

  • Jami'an 'yan sanda a Bayelsa sun kama wasu mutane uku da ake zargin sun yi wa wani matashi taron dangi da kashe shi har lahira
  • Ana zargin mutanen ne uku da kashe matashi dan shekara 32 mai suna Ebimotimi Freeborn bisa zargin cewa ya saci biredi
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Asinim Butswat ya ce an kama wadanda ake zargin a ranar 9 ga watan Yuli a Yenagoa

Jihar Bayelsa - Rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ta cafke wasu mutane uku da ake zargin daukar doka a hannu.

Ana zargin wadannan mutane uku da kashe wani matashi Ebimotimi Freeborn kan zargin satar biredi.

'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Mutane 3 Kan Kashe Matashi Bisa Zargin Satar Biredi
Rundunar 'Yan Sanda Na Zargin Mutane 3 Da Kashe Matashi Bisa Zargin Satar Biredi. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Asinim Butswat shi ya bayyana haka inda ya ce an kashe matashin mai shekaru 32 a ranar 9 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

'Ba Mu San Laifin Da Muka Aikata Ba', Wadanda Ake Zargin Yan Boko Haram Da Ke Tsare A Barikin Giwa

Yadda mutane ukun suka kashe matashin bisa zargin satar biredi

Wadanda ake zargin sun hada da Preye Mathew mai shekaru 50 da Theophilus Tiro mai shekaru 28 da kuma Famous Precious mai shekaru 22, TheCable ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Butswat ya ce an kama mutanen uku ne a ranar 9 ga watan Yuli da misalin karfe 5 na yamma akan hanyar Tombia- Amassoma, cewar ThisDay.

'Yan sanda sun gargadi jama'a kan daukar doka a hannu

Tribune ta tattaro cewa kakakin rundunar ya yi Allah wadai da irin wannan mummunan aika-aika inda ya gargadi al'umma da su guji daukar doka a hannunsu don gudun fushin hukuma.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna amsa tambayoyi a ofishin hukumar inda ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kara karanta wannan

An Samu Matsala: Bene Mai Hawa Uku da Ake Tsaka Ya Aiki Ya Rushe, Bayanai Sun Fito

A Najeriya, mutane na yawan daukar doka a hannunsu musamman abin da yafi sata da ke faruwa a yankuna, hakan ya sabawa dokokin kasa kamar yadda ya ke a cikin kundin tsarin mulki.

Kotu Ta Tsare Matashi Bisa Zargin Satar Jaririya ’Yar Watanni 2

A wani labarin, kotu majistare da ke zamanta a Yenagoa da ke jihar Bayelsa ta tsare wani matashi da ake zargi da satar jaririya.

Matashin mai suna Solomon Kingley ya saci jaririyar ce da ba ta wuce watanni biyu ba a duniya a birnin Yenagoa.

Solomon ya fadawa jami'an tsaro cewa sun taba yin mu'amala da mahaifiyar jaririyar a otal amma ya gane cewa ba 'yarsa ba ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.