'Yan Bindiga Sun Halaka 'Yan Sanda Hudu a Wani Harin Kwanton Bauna a Jihar Zamfara
- Ƴan bindiga sun halaka jami'an ƴan sanda mutum huɗu a cikin ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara
- Ƴan bindigan sun yi wa jami'an ƴan sandan kwanton ɓauna ne suna tsaka da aikinsu a cikin tsakar dare
- Miyagun ƴan bindigan sun kuma farmaki wani ƙauye a yankin inda suka saci shanu masu yawan gaske
Jihar Zamfara - Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da halaka jami'anta huɗu da ƴan bindiga suka yi a wani hari ranar Litinin da daddare a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar.
Jami'an ƴan sandan sun sanya shingen bincike ne akan titin hanyar Bungudu-Gusau lokacin da ƴan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna suka buɗe musu wuta, jaridar Leadership ta rahoto.
Channels tv ta ambato kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, yana tabbatar da aukuwar harin a ranar Talata da safe.
"Mun je wurin da safen nan inda muka tabbatar da cewa an halaka jami'an mu mutum huɗu a harin. Suna cikin sintiri ne a wajen da suka saba sanya shingen bincike kafin su ƙara matsawa wani wurin lokacin da ƴan bindigan suka mamaye su." A cewarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ƴan bindigan sun kuma farmaki wani ƙauye a yankin
Tun da farko wani mazaunin garin Bundugu, Ibrahim Bungudu ya bayyana cewa ƴan sanda huɗu ne aka halaka a yayin harin.
Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma harbi wani mutum ɗaya a ƙauyen Tagero cikin yankin Furfuri na ƙaramar hukumar Bungudu.
Ibrahim ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da shanu masu yawa na mutanen ƙauyen Tagero.
"Ƴan bindigan sun yi wa jami'an ƴan sandan kwanton ɓauna ne akan titin Gusau-Bungudu kusa da kamfanin Nabature inda suka halaka mutum huɗu. Sun kuma sace shanu masu yawa a ƙauyen Tagero da ke a yankin Furfuri sannan sun harbi mutum ɗaya a hannu a ƙauyen." A cewarsa.
Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Cikin Dare a Arewacin Najeriya, Rayukan Mutane Da Yawa Sun Salwanta
Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga a Zamfara
A wani labarin kuma dakarun sojojin Najeriya sun sheƙe ƴan bindiga mutum huɗu a wani farmaki da suka kai maɓoyarsu a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun kuma ceto wasu mutane masu yawa da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su da ke tsare a hannunsu.
Asali: Legit.ng