Aikin Hajji: Rukunin Farko Na Alhazan Legas Sun Baro Saudiyya Zuwa Najeriya

Aikin Hajji: Rukunin Farko Na Alhazan Legas Sun Baro Saudiyya Zuwa Najeriya

  • An bayyana cewa rukunin farko na alhazan jihar Legas sun baro birnin Jeddah zuwa Najeriya
  • Alhazan sun baro Saudiyya ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Litinin, inda ake sa ran isowarsu Legas da misalin ƙarfe 03:30 na yamma
  • An bayyana cewa jirgin na musamman ne da ya ɗauko tsofaffi da kuma masu fama da rashin lafiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jeddah, Saudi Arabia - Aƙalla alhazai 380 na jihar Legas da suka gudanar da aikin hajji ne aka tabbatar da tasiwarsu daga ƙasar Saudiyya zuwa Najeriya.

An bayyana cewa alhazan sun baro filin tashi da saukar jirage na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da misalin ƙarfe 11:30 na safe a agogon ƙasar Saudiyya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Alhazan Legas sun baro kasa ma tsarki
Rukunin farko na alhazan jihar Legas sun baro kasa mai tsarki. Hoto: Salaam Lateef
Asali: Facebook

Ana sa ran isowarsu filin tashi da saukar jirage na Murtala Mohammed da ke birnin Legas da misalin ƙarfe 03:30 na yamma a agogon Najeriya.

Kara karanta wannan

Na Yi Wa Jam'iyyar APC Kamfe Amma Ta Bani Kunya, Fittaciyar Jarumar Fina-Finai Na Najeriya

Jirgin ya ɗauko tsofaffi da alhazai marasa lafiya

Shugaban alhazan jihar Legas, Prince Anofiu Elegushi, ya bayyana cewa jirgin na musamman ne wanda ke ɗauke da tsofaffi da kuma masu fama da rashin lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa jirgin na ɗauke da da maza 185 da kuma mata 195, waɗanda AbdulWaheed Shonibare, mamba a hukumar jin daɗin alhazan jihar ke jagoranta.

A yayin da yake musu fatan sauka lafiya, Elegushi ya yi kira ga alhazan da su yi ƙoƙarin kiyaye faɗawa aikata saɓon Ubangiji domin ci gaba da zama ba tare da wani zunubi ba.

An buƙaci alhazan su nuna kyawawan dabi'u idan suka koma gida Najeriya

Elegushi ya kuma yi kira ga alhazan da su yi ƙoƙarin nuna irin aikin da suka yi a ƙasa mai tsarki, ta hanyar mu'amalantar mutane da kyawawan ɗabi'u idan suka dawo gida Najeriya.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

Haka nan ya bai wa sauran alhazan da ke can haƙuri, inda ya basu tabbacin cewa za a maida kowa gidan nan ba da jimawa ba, kamar yadda The Guardian ta yi rahoto.

Elegushi ya kuma shawarci alhazan da su kiyayi wuce ƙa'idar kayan da aka ba su damar ɗaukowa, sannan ya kuma shawarcesu da kar su ɗauko ruwan Zam-Zam cikin jakunkunansu.

Mahajjaciya ta mayar da miliyan 56 da ta tsinta a Saudiyya

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata mahajjaciya mai suna A'ishatu da ta mayar da maƙudan kuɗaɗe da ta tsinta zuwa hukumar alhazan jiharta.

A'ishatu, wacce take cikin rukunin alhazan jihar Zamfara, ta tsinci kuɗaɗe $80,000, kwatankwacin naira miliyan 56 a kuɗin Najeriya, waɗanda ta mayar zuwa hukumar alhazan jihar ta Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng