Wasu Kungiyoyi Sun Bukaci a Sanya Ido Kan Ganduje Kada Ya Gudu Daga Kasar Nan

Wasu Kungiyoyi Sun Bukaci a Sanya Ido Kan Ganduje Kada Ya Gudu Daga Kasar Nan

  • Wata ƙungiya da ke fafutuƙar yaƙi cin hanci da rashawa ta buƙaci hukumar shige da fice da ƴan sandan ƙasa da ƙasa su sanya ido kan Ganduje
  • Ƙungiyar ta yi nuni da cewa tsohon gwamnan na jihar Kano na iya sulalewa ya ba r ƙasar nan saboda binciken da ake masa
  • Sai dai ɓangaren tsohon gwamnan ya yi zazzafan martani kan kiran da ƙungiyar ta yi na a sanya ido kan Ganduje

Jihar Kano - Gamayyar wasu ƙungiyoyi a ƙarƙashin Movement Against Corruption in Nigeria (MACIN), ta yi kira ga hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) da Interpol su sanya ido kan tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, domin kada ya gudu ya bar ƙasar nan.

Jaridar Daily Trust tace ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da manema labarai a sakatariyar ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) a birnin Kano ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bayyana Matakan Da Zai Dauka Wajen Murƙushe Matsalar Tsaro a Mulkinsa

An bukaci NIS da Interpol su sanya ido kan Ganduje
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban ƙungiyar Kabiru Saidu Dakata ya buƙaci NIS da Interpol su sanya ido kan Ganduje saboda yana ɓoyewa a bayan Shugaba Tinubu domin kada a cafke shi inda daga bisani zai yi ƙoƙarin sulalewa daga ƙasar nan.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Ganduje da mutunta doka ya kai kansa wajen hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar domin a bincike shi, cewar rahoton Tribune.

Ɓangaren Ganduje ya yi martani

Da yake martani kan kiran da ƙungiyar ta yi, tsohon kwamishinan watsa labarai a gwamnatin Ganduje, Malam Muhammad Garba, ya yi fatali da kiran da ƙungiyar ta yi na Shugaba Tinubu ya nesanta kansa da tsohon gwamnan.

Garba ya bayyana cewa shugaban ƙungiyar, Kabiru Saidu Dakata, wanda ɗan jam'iyyar PDP ne ya koma NNPP a yanzu yana fakewa ne da ƙungiyar kawai domin caccakar gwamnatin Ganduje da ta gabata.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Yi Galaba Kan 'Yan Ta'adda Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace a Jihar Arewa

Ya ƙara da cewa ba a daɗe ba da jin Dakata a kafafen watsa labarai yana neman samun muƙami a gwamnatin NNPP ta jihar Kano, inda aka ɗauki nauyinsa ya bayyana a gidan talbijin na Arise TV domin goyon bayan rusau ɗin da gwamnatin NNPP ta ke yi a Kano.

An Dakatar Da Gayyatar Da PCACC Ta Yi Wa Ganduje

A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Kano Aɓdullahi Umar Ganduje ya samu nasara kan hukumar yaƙi da rashawa da karɓar ƙorafe-ƙorafe (PCACC) ta jihar.

Wata kotu ta dakatar da hukumar daga gayyata ko cin zarafin tsohon gwamnan kan bidiyonsa na cusa dala a aljihunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng