Ido Zai Raina Fata: Majalisa Za Tayi Binciken Yadda Aka Saida Kadarorin Gwamnati
- Bincike-binciken da za ayi a majalisar tarayya zai shafi saida kadarorin gwamnati da aka yi a Najeriya
- Akwai hukumomin da sun yi gwanjon dukiyoyi gwamnati, kuma ana zargin hakan bai bi ka’idoji ba
- ‘Yan majalisar wakilan za su duba aikin ITF ganin cewa kamfanoni ba su aiki da dokar hukumar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta ce za ta fara bincike a kan yadda aka saida kadarorin gwamnati ba tare da ka’ida ba tun daga 2010 zuwa 2022.
Rahoton The Nation ya ce ‘yan majalisar kasar za su yi bincike game da yadda kudin da aka samu wajen cefanar da kadarorin ba su shiga baitul-mali.
Ana zargin abin da ke kai wa asusu bai kai ya kawo ba, idan aka kamanta da adadin kudin da aka saida wadannan kadarori da gwamnatin ta mallaka.
Za a duba sha'anin ITF
Majalisar wakilan kasar ta yanke shawarar gudanar da bincike na musamman a kan ayyukan ITF domin gano abubuwan su ka hana hukumar samun nasara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata matsaya da aka cin ma shi ne rashin aiki da doar ITF a kamfanoni daga 2010 zuwa yanzu.
Rahoton ya ce an cin ma wannan matsaya ne a sakamakon koken da aka kai, sai ‘yan majalsar tarayyar su ka bukatar a kafa kwamitoci da za su yi bincike.
Inda ake zargin an yi badakala
Oluwole Oke (PDP, Osun) ya na zargin cewa saida kadarorin gwamnati da aka yi a hukumomin NPA na tashoshin ruwa da NIMASA ya sabawa dokar kasa.
Honarabul Oke ya ce an yi irin wannan gwanjo da dukiyar al’umma ba a kan ka’ida ba a hukumar NRC mai kula da jiragen kasa da hukumar kwastam ta NCS.
The Cable ta ce binciken zai shafi RMDA wanda ita ce hukumar kula da cigaban gabobin teku.
Za a kafa kwamitoci na musamman da za su gudanar da wannan aiki ne idan an rantsar da sauran kwamitocin majalisa, sai a ba su lokacin da za su kawo rahoto.
Kundin tsarin mulki ya yi tanadi kan yadda za a saida kadarorin gwamnati a dokar kula da tattalin arziki ta 2009 da dokar sayo kaya a gwamnati ta shekarar 2007.
Akwai sabani a Majalisar NWC
Kwanan nan aka ji shugabannin jam’iyyar APC da 'Yan Majalisa sun samu ja-in-ja a kan batun mukaman da aka raba a majalisar tarayya da kuma ta dattawa.
Yanzu labari ya zo cewa ana Abdullahi Adamu ya hana sauran majalisar NWC ganin rahoton binciken kudi da aka yi, sa kuma aka ji an dakatar da taron NEC.
Asali: Legit.ng