Kyakkyawar Budurwa Ta Zolayi Mai Gadi, Ta Ce Ya Biyo Ta Su Yi Nishadi, Martaninsa Ya Ba da Mamaki
- Wata ‘yar Najeriya ta zolayi wani mai gadi a lokacin da ta fita cefane a kantin siyayya, ta nemi ya bi ta
- Mutumin ya fada tarkon matar, inda yace a shirye yake ya bi ta don su yi nishadi tare, duk da zolayarsa ta ke
- Mutane da yawa sun fashe da dariya a lokacin da matar tace ba fa da shi take ba, kawai waya take bai sani ba
Wata budurwa ‘yar Najeriya ta yi wasa da zuciyar wani mai gadi a lokacin da ta zolaye shi a kantin siyayya, ta ce ya bi su yi nishadi.
A lokacin da ta matsa kusa da mutumin, budurwar mai suna da @king__michy ta tambaye shi ko zai tafi tare da ita.
Ta ce:
“Shin za mu iya cancarewa tare?”
“Sharadi Ba Za Ka Yi Mun Kishiya Ba”: Budurwa Ta Yi Alkawarin Baiwa Duk Wanda Ya Aureta Gida, Mota da Miliyan 50 a Bidiyo
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kyakkyawar budurwa a kantin siyayya
Mutumin sai da ya sake tambayar budurwar abin da ta fada, inda ta tabbatar da abin da ta fada da fari da karin tambayoyi.
Nan take ya amsa da ya amince su tafi don yin nishadi da cancarewa tare.
A lokacin da mutumin ya amsa, sai ta fitar na’urar sauraran sauki a kunne, tace masa ai ba da shi take ba, waya take.
Haka dai ya ji kunya, gwiwarsa ta yi sanyi ya fice daga inda budurwar ke daukar bidiyo.
Martanin jama’a
A kasa, Legit ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa bayan ganin bidiyon a kafar sada zumunta.
Marho:
“Kamata ya yi ki rufe fuskarsa mana.”
feyisayo ajons:
“Amma kin yaudari wannan mutumin. Idan matarsa ta ga wannan to akwai matsala.”
Ramat Fumi:
“Mutumin bai gane bane.”
iam_aweni021:
“Kai amma na jiwa wannan mutumin.... ya zo a ji dadi tare dashi.”
kisskeed:
“Mutumin har ya bata rai gaba daya.”
georgeogonaya:
“Ba wani abu bane ai, akwai hanyoyin nishadi da yawa.”
cywilliams:
“Kada ki jefa aikin wannan mutumin a hadari, don Allah.”
oppy moore:
“Ya fi kyau mutumin nan ya kwana a can kada ya koma gida.”
StallionBlxxx:
“Nan kusa za su kafta miki mari sai na’urar ta fita.”
jazpal:
“A gasken gaske idan yana da kudi, za ku yi nishadi. To meye a nan.”
Mata ta saki bayanan katin ciran kudin saurayinta a Twitter don ta yi maganinsa
Wata budurwa mai suna Chloe a shafin Twitter ta saki bayanan katin cire kudi na saurayinta a dandalin sada zumunta da muhawara a yunkurinta na yin maganinsa.
A cewar Chloe, saurayin nata ya ci amanarta kuma hakan ne ma ya kai ga ta aikata yada bayanan katin. Ta bukaci kowa da ya ga katin ya yi siyayya da shi a kantunan yanar gizo.
Mutane da yawa sun bi abin da ta fada, inda suka yi siyayya tare da bayyana abin da suka siya da kuma yabawa saurayin. Ta ce duk ranar Lahadi ake biyansa a wurin aiki.
Asali: Legit.ng