Tsohon Mataimakin Sufetan 'Yan Sanda Ya Bukaci Tinubu YaYi Fatali Da Shawarar Yin Sulhu Da 'Yan Bindiga
- Tsohon mataimakin sufetan ƴan sanda ya shawarci Shugaba Tinubu da kada ya hau teburin sulhu da ƴan bindiga
- Ambrose Aisabor ya buƙaci shugaban ƙasar da ya yi kunnen uwar shegu da shawarar da Ahmed Sani Yarima ya bayar na a tattauna da ƴan bindiga
- A cewarsa tattaunawa da ƴan bindiga za ta nuna cewa a jami'an tsaron ƙasar nan sun gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma
Benin - Tsohon mataimakin suferan ƴan sanda na ƙasa, Ambrose Aisabor, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya yi fatali da shawarar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yarima ya bayar na ayi sulhu da ƴan bindiga.
Aisabor ya yi wannan kiran ne a yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust ta wayar tarho a birnin Benin ranar Asabar.
Mmesoma Ejikeme Ta Sharbi Kuka a Yayin Wayar Tarho, Ta Dauki Alkawarin Bayar Da Hakuri, Sabon Bidiyo Ya Bayyana
Tsohon mataimakin sufetan ƴan sandan ya yi kalaman ne domin martani kan kiran da Ahmed Sani Yarima ya yi na a zauna kan teburin sulhu da ƴan bindiga.
Matsalar tattaunawa da ƴan bindiga, Aisabor
Ya bayyyana cewa tattaunawa da ƴan bindigar zai nuna cewa jami'an tsaron ƙasar nan sun gaza, kuma basu da kayan aikin da za su iya murƙushe ƴan bindigan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Lokacin da Yarima ya ziyarci Shugaban ƙasa, ya ba shi shawarar yakamata a hau teburin sulhu da ƴan bindigan da ke Najeriya, musamman na yankin Arewa maso Yamma domin yi wa waɗanda suka tuba daga cikinsu afuwa."
"Yarima ya danganta abinda ya faru a Niger Delta da ƴan bindiga. Basu da alaƙa saboda tsagerun Niger Delta suna fafutuka ne domin a inganta musu yankinsu saboda lalacewar da yake yi a dalilin haƙo man fetur da ake yi a yankin."
"Mun Same Shi Lullube Da Zuma": Mahaifin Jaririn Da 'Yan Bindiga Suka Halaka Mahaifiyarsa Ya Bayyana Yadda Ya Rayu Sa'o'i 24 Bayan Ta Rasu
Ya bayyana cewa tsagerun Niger Delta ba sa garkuwa da mutane ko halaka su amma ƴan bindiga suna garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma, inda ya ƙara da cewa ƴan bindiga har yanzu basu fito sun bayyana wa ƴan Najeriya abinda ya sanya su ɗaukar makamai ba, cewar rahoton Businessday.
Aisabor ya yi nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Katsina, har sulhu ya yi da ƴan bindigan amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba, inda suka ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Talauci Da Jahilci Ya Kawo 'Yan Bindiga, Ahmed Yarima
A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura, ya bayyana muhimman abubuwa biyu da suka assasa samuwar ƴan bindiga a Arewacin Najeriya.
Ahmed Sani Yarima ya yi bayanin cewa talauci da jahici su ne suka janyo matsalar ƴan bindiga ta yi ƙamari a Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng