Matar Da Ta Fi Kowa Tsufa Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ta Rasu
- Allah ya yi wa matar da ta fi kowa tsufa cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 63 da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a bara, rasuwa
- Marigayiya Hajiya Halimatu Attah ta rasu ne a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli tana da shekaru 85 a duniya
- Daya daga cikin 'ya'yanta Abdulmalik Attah ya tabbatar da rasuwar mahaifiyar tasu, ya kuma ce bata yi fama da kowani rashin lafiya ba
Kaduna - Matar nan da ta fi kowa tsufa cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 63 da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Maris din 2022, ta rasu tana da shekaru 85 a duniya.
Hajiya Halimatu Attah ta rasu a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli da misalin karfe 6:20 na yamma a Kaduna kamar yadda wani danginta ya bayyana.
Ta rasu ba tare da ta kwanta rashin lafiya ba
An yi garkuwa da marigayiyar wacce ta fito daga shahararran gidan nan na Attah tare da diyarta bayan sun dawo daga ganin likita a birnin Alkahira a shekarar da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tabbatar da mutuwarta ga jaridar Daily Trust a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, daya daga cikin 'ya'yanta, Abdulmalik Attah, ya ce shekarun mahaifiyar tasu 86 kuma ta rasu ba tare da kowani rashin lafiya ba.
Ya ce za a tuna da ita saboda alkhairinta, kasancewar ta kasance uwa daya tamkar da dubu sannan tana yi wa kowa fatan alkhairi ba wai yaranta kawai ba.
Abdulmalik Attah ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta kula da kowa a matsayin nata ba tare da shamaki ba.
Da aka tambayesa ko akwai wani da ta fada masa game da halin da ta shiga a sansanin yan fashi da zai dunga tunawa a kodayaushe, ya tuna yadda ta dage kan tabbatar da sakin sauran mutane cikin koshin lafiya, yayin da yake nuna godiyarsa ga cikar burinta.
Mahajjaciyar Najeriya ta tsinci miliyan 56 a kasar Saudiyya, ta mayarwa mahukunta
A wani labarin, mun ji cewa wata mahajjaciyar Najeriya daga karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, Aishatu y’an Guru Nahuce, ta tsinci kudi har dala 80,000 a kasar Saudiyya.
Hajiya Aishatu wacce Bafullatana ce bata yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da kudin wanda yawansu ya kai naira miliyan 56 a kudin Najeriya ga mahukunta.
Asali: Legit.ng