DSS Ta Yi Ram Da Abdulaziz Yari, An Taso Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara a Gaba
- Jigo a r APC, Abdulaziz Yari ya na hannun jami’an DSS tun kwanaki kusan uku da suka wuce
- Hukumar DSS masu fararen kaya sun aikawa tsohon Gwamnan na jihar Zamfara goron gayatta
- Yari ya tsaya takarar shugabancin majalisar dattawa, ya ja da matakin da jam’iyya ta dauka
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ya na hannun jami’an hukumar DSS masu fararen kaya a Najeriya.
Punch ta ce zuwa yanzu babu wanda ya san dalilin tsare Abdulaziz Yari mai wakiltar Zamfara ta yamma a majalisar dattawan kasar nan.
Wata majiya ta ce Yari ya kai kan shi zuwa ofishin hukumar DSS bayan zaman majalisar tarayya da aka yi a ranar Alhamis da ta wuce.
Hakan ya na zuwa ne bayan jami’an tsaron sun aikawa fitaccen ‘dan siyasar goron gayyata kamar yadda wani na kusa da shi ya shaida.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Sanata Abdulaziz Yari ya na hannun DSS, amma da yardar Ubangiji ba zai dade ba zai fito.
Ya je ofishinsu ne bayan zaman majalisa. Ni na yi masa rakiya kuma har yanzu ya na can."
- Majiya
Meya faru aka kama Yari?
A wani rahoto da ya fito daga Peoples Gazette, ana zargin cewa DSS ta cafke Sanata Yari ne saboda ya ki amsa wayar shugaban hukumar.
Akwai kuma rahotannin da ke cewa shugaban kasa ya kira ‘dan siyasar ta waya amma ya ki dauka, sai dai Legit.ng Hausa ba ta tabbacin labaran.
Rahoton The Nation ya nuna jami’an DSS sun bukaci ganin Yari ne saboda yana neman kawowa Godswill Akpabio cikas a majalisar dattawa.
Zargin adakalar kudin kamfe
Sahara Reporters ta ce ‘dan siyasar ya samu kan shi a matsala ne bisa zargin Gwamnan CBN ya ba shi N45bn domin yakin neman zabe a 2019.
Idan labarin ya tabbata, Yari a lokacin ya na Gwamna ya na da hannu wajen wata badakalar kudi da aka tafka domin tazarcen Muhammadu Buhari.
Da aka nemi tuntubar tsohon Gwamnan ta salula a ranar Asabar, an ji wayarsa ta na kashe.
'Yan majalisa za su yi bincike
A makon jiya rahoto ya fito cewa binciken da za a fara a Majalisar tarayya za su shafi Gwamnatocin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari.
Kwamitocin Majalisar za su gano gaskiyar Naira Tiriliyan 2.3 da aka wawura a karkashin Hukumar TETFund da badakalar albashi a tsarin IPPIS.
Asali: Legit.ng