Mahaifin Dalibai Mmesoma da Ta Yi Karyar Cin JAMB Ta Fito Ya Ba Hakuri

Mahaifin Dalibai Mmesoma da Ta Yi Karyar Cin JAMB Ta Fito Ya Ba Hakuri

  • Rahoton da muke samu daga NTA ya bayyana cewa, mahaifin dalibar da ta yi kwange a JAMB ya ba da hakuri
  • Ya bayyana gaskiyar abin da ya faru, inda yace bai yi zaton ‘yarsa za ta aikata wannan aikin ba
  • A baya, ‘yan Najeriya sun nuna damuwa kan yadda hukumar JAMB ta janye sakamakon dalibar

Jihar Anambra - Mista Romanus Ejikeme, mahaifin Mmesoma Ejikeme, dalibar da ta jirkita sakamakon jarrabawarta na JAMB, ya fito fili ya nemi gafarar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) da ma ‘yan Najeriya baki daya.

Kamar yadda aka gani a wata hira da gidan talabijin na Najeriya (NTA), ya ce da far dai ‘yarsa ta shirga masa karya don haka yanzu da ya san gaskiya, yana fatan JAMB ta yafewa ‘yarsa.

Kara karanta wannan

Aisha Yesufu Ta Nemi a Hukunta Tinubu Kamar Yadda Aka Yi Wa Mmesoma

A baya, yarinyar ta yi ikirarin cewa, ta lashe sakamako mafi yawa na UTME na 2023, lamarin da ya jawo cece-kuce bayan da hukumar JAMB ta ce ba haka bane.

Mahaifin Mmesoma ya nemi afuwar daliba
Mahaifin Mmesoma sadda yake ba da hakuri | Hoto: NTA
Asali: Facebook

JAMB ta janye sakamakon daliba

Daga bisani, an janye sakamakon da ta samu na maki 249, bayan ta yada cewa, ta samu maki 362.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

JAMB ta bayyana cewa, tabbas tana da hujjar cewa yarinyar ta jirkita sakamakon ne, kana ba wannan ne karon farko da matasa ke yin haka ba.

Hakan ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin hukumar na da matsalar sauya sakamakon

Ta amsa cewa ta jikita sakamakon

A yau ne aka samu labarin cewa, dalibar ta bayyana gaskiya, inda tace da kanta ta jirkita sakamakon jarrabawar.

Wannan na fitowa ne daga wani kwamitin da gwamnan jihar Anambra ya hada, inda suka titsiye yarinyar tare da jin gaskiyar abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Ya Kamata a Bari Mmesoma Ta Samu Gurbin Karatu a Jami’a: Tsohon Ministan Buhari, Ya Fadi Dalili

Ya zuwa yanzu, labarin ya sauya domin dalibar da ake ganin ba a yi mata adalci ba ta tabbatar da aikata laifi mai kama da satar amsa.

Mahaifinta ya nemi afuwa

Da yake zantawa da NTA, ya bayyana cewa:

“Diya ta bata bayyana min gaskiya a kan lokaci ba; lokacin da na gano laifinta, na daura mata laifin.
“Na mata kashedin cewa, Mmesoma ki bi a hankali; kinsan ke tauraruwa ce kuma zai dishashe ki.
“Amma ina ba JAMB da ‘yan Najeriya hakuri a matsayi na na uba a yafe mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.