Mmesoma: “Ta Yi Amfani Da Wayarta”, Da Wasu Abubuwa 3 Da Kwamitin Binciken Anambra Ya Gano
- Kwamitin bincike da gwamnatin jihar Anambra ta kama domin gano gaskiya a takaddamar makin da Miss Ejikeme Joy Mmesoma ta samu ya nuna bata da gaskiya
- A cewar kwamitin, sakamakon da Mmesoma ke ikirarin nata ne da maki 362 na bogi ne
- Mmesoma ta yarda cewa ta yi kutse a sakamakon jarrabawarta na UTME, don haka ta yaudari iyayentam makaranta da kuma gwamnatin jihar
Nnewi, jihar Anambra - Kwamitin bincike da gwamnatin jihar Anambra ta kafa domin binciken takaddamar da ke kewaye da sakamakon jarrabawar UTME na Mmesoma Joy Ejikeme ya gano wasu abubuwa.
A rahoton kwamitin, ya rubuta cewa “Ejikeme Joy Mmesoma" ta yarda cewa da kanta ta kirkiri sakamon na bogi ta hanyar amfani da wayarta," jaridar Leadership ta rahoto.
Mmesoma ta yarda ta kirkiri sakamakon JAMB, sakamakon binciken kwamitin gwamnati ya bayyana
A bisa takardar da tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili ta saki a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, kwamitin gwamnatin Anambra ya gano wasu abubuwa hudu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ezekwesili ta janye goyon bayanta ga Mmesoma sannan ta jinjinawa hukumar JAMB, Daily Trust ta rahoto.
Abu na 1 da aka gano: Sakamakon jarrabawar da hukumar JAMB ta saki dangane da yawan makin da Ejikeme Joy Mmesoma ta samu a UTME ya kasance 249.
Abu na 2 da aka gano: Sakamakon jarrabawar da Ejikeme Joy Mmesoma ke nunawa a matsayin nata da maki 362 na bogi ne kamar yadda banbancin da aka samu a lambar rajista, ranar haihuwa, sunan wajen jarrabawa da sauran abubuwa suka nuna.
Abu na 3 da aka gano: Ejikeme Joy Mmesoma ta yarda cewa ita ta kirkiri sakamakon jarrabawar na bogi da kanta, ta hanyar amfani da wayarta.
Abu na 4 da aka gano: Shugabar makarantar Anglican Girls' Secondary School - Misi Edu Uche da sakataren ilimi na darikar Anglican da ke Nnewi sun nuna takaicinsu kan abun da Ejikeme Joy Mmesoma ta aikata.
Aisha Yesufu ta nemi a hukunta Tinubu kamar yadda JAMB ta yi wa Mmesoma
A wani labarin kuma, shahararriyar yar fafutuka, Aisha Yesufu, ta ce Mmesoma Ejikeme ta sauya sakamakon jarrabawa ne kamar yadda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a lokacin zaben watan Fabrairun 2023.
Da take rubutu a shafinta na Twitter, Yesufu ta bayyana cewa ya kamata a hukunta shugaban kasa Tinubu sannan a tsige shi daga ofis kamar yadda hukumar JAMB ta hukunta Mmesoma.
Asali: Legit.ng