Kwamitin Bincike Ya Bayyana Abinda Yakamata Ya Faru Da Mmesoma Ejikeme Bayan Ta Kara Makin JAMB
- Daga ƙarshe Mmesoma Ejikeme ta bayyana cewa ta ƙara makinta na jarabawar share fagen shiga jami'a (UTME)
- Wani kwamiti mai zaman kansa da gwamnatin jijar Anambra ta kafa ya bayyana hakan a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli
- Kwamitin ya bayar da wasu shawarwari domin tabbatar da cewa yarinyar mai shekara 19 a duniya ta tafiyar da rayuwarta yadda ya dace bayan wannan rikicin
Nnewi, jihar Anambra - Kwamitin mutum takwas da gwamna Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya kafa domin bincikar badaƙalar da ke tattara da sakamakon jarabawar share fagen shiga jami'a (UTME) na Mmesoma Ejikeme, ya bata sabon umarni.
Kwamitin ya buƙaci Mmesoma Ejikeme da ta ba hukumar shirya jarabawar shiga jami'a (JAMB) haƙuri kan aika-aikar da ta tafka, cewar rahoton The Punch.
Wakilan na gwamnati sun kuma shawarci Mmesoma da ta je a duba lafiyarta da bata shawarwari, kamar yadda rahoton Premium Times ya tabbatar a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli.
Zance Ya Ƙare: Kwamitin Binciken da Gwamna Ya Kafa Ya Gano Gaskiya Kan Ɗalibar Da Ake Zargi da Ƙara Makin JAMB
Kwamitin ya buƙaci Mmesoma Ejikeme da ta bayar da haƙuri
Rahoton kwamitin binciken mai shafi takwas ya kuma bayar da shawara cewa Mmesoma ta gaggauta rubuta takardar bayar da haƙuri ga makarantarta (Anglican Girls’ Secondary School, Uruagu Nnewi), da gwamnatin jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mmesoma ts zama abin magane ne bayan iƙirarin da ta yi cewa ta samu maki 362 a jarabawar share fagen shiga jami'a (UTME) a maimakon maki 249 da hukumar JAMB ta haƙiƙance cewa shin ne makinta da ta samu.
Badaƙalar sakamakon na Mmesoma dai ya kawo ruɗani musamman a kafafen sada zumunta inda wasu suke goyon bayanta da ganin cewa JAMB ba ta yi mata adalci ba, yayin da wasu ke goyon bayan hukumar JAMB bayan ta fallasa ta.
Kwamitin Anambra Ya Tabbatar da Laifin Mmesoma Na Kara Makin JAMB
Rahoto ya zo kan yadda gaskiya ta bayyana dangane da ruɗanin sakamakon jarabawar share fagen shiga jami'a na ɗaliba Mmesoma Ejikeme wanda ake ta taƙaddama a kansa.
Kwamitin binciken da gwamnan jihar Charles Soludo ya kafa domin gano gaskiga ya tabbatar da cewa ɗalibar ita ce ta shirya kitimurmura ta ƙara wa kanta maki da kanta.
Asali: Legit.ng