Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutum 24 Daga Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi mummunan bata kashi da ƴan bindiga a dajin Kabugu Lamba da ke a jihar Zamfara
- A yayin bata kashin dakarun sojojin sun halaka ƴan bindiga mutum hudu da jikkata wasu da dama daga cikinsu
- Jajirtattun dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ceto wasu mutum 24 da su ke a tsare a hannun ƴan bindigan
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Operation Hadarin Daji sun ceto mutum 24 da ƴan bindiga suka sace a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, a ranar Juma'a, 8 ha watan Yulin 2023.
Sumamen da dakarun sojojin suka kai a maɓoyar ƴan bindigan ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu akan inda ƴan bindigar ke ɓoye a dajin Kabugu Lamba, cewar rahoton The Cable.
A cewar rahotan Channels tv, dakarun sojojin sun yi musayar wuta da ƴan bindigan, wanda hakan ya sanya suka ranta ana kare suka bar mutanen da su ke riƙe a hannunsu.
Ƴan bindiga mutum huɗu ne dai aka halaka a yayin artabun da dakarun sojojin yayin da sauran suka gudu ɗauke da miyagun raunikan bindiga.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutanen da aka ceto ɗin sun haɗa da manyan maza mutum 14, jariri ɗaya da mata mutum tara, waɗanda tuni aka miƙa su a hannun hukumomin da suka dace domin haɗa su da iyalansu.
Ƴan sanda sun ceto yaran da ƴan bindiga suka sace a Zamfara
Wannan na zuwa ne dai bayan ƴan sanda sun ceto wasu yara tara da ƴan bindiga suka sace a ƙauyen Goron-Namaye cikin ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Ƴan bindigan dai sun yi awon gaba da yaran ne lokacin da su ke kan hanyarsu ta zuwa samo makamashi a cikin daji.
Bello Turji Ya Sako Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yaransa Suka Sace
A wani labarin na daban kuma, ƙasurgumin shugaban ƴan bindigan da ya addabi jihar Zamfara, Bello Turji ya sako wasu daga cikin mutanen da yaransa suka sace a jihar Zamfara.
Hatsabibin shugaban na ƴan bindigan dai ya sako mutum 20 daga cikin waɗanda yaransa suka yi garkuwa da su, ciki har da wata amarya wacce sati ɗaya da ɗaura mata aure aka yi garkuwa da ita.
Asali: Legit.ng