Matar Aure, Maimuna Suleiman, Ta Daba Wa Mijinta Wuka Har Lahira a Jihar Bauchi
- Maimunatu Sulaiman yar shekara 21 a duniya ta caka wa mijinta wuƙa har lahira a Anguwar Kofar Dumi, jihar Bauchi
- Hukumar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami'anta sun kama wacce ake zargi domin gudanar da bincike
- Bayanai sun nuna cewa wata yar cacar baki ta shiga tsakanin ma'auratan har ta kai ga mijin, Aliyu Muhammed ya rasa ransa
Jihar Bauchi - Wata mata yar kimanin shekara 21 a duniya, Maimuna Suleiman ta shiga hannu bisa zargin halaka mijinta Aliyu Mohammed ta hanyar daɓa masa wuka a jihar Bauchi.
Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin a Anguwar Ƙofar Dumi, Bauchi, ta ce a halin yanzun wacce ake zargin na tsare.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan, ASP Aminu Gimba Ahmed, ya ce suna kan bincike kan ainihin abinda ya faru, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce bayan samun rahoton abinda ya faru ranar 5 ga watan Yuli, dakarun 'yan sanda suka garzaya Kofar Dumi, suka kama Maimunatu Sulaiman bisa zargin kisan kai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kakakin yan sanda ya ƙara da cewa da farko jami'ai sun ɗauki Maimunatu da Mamacin zuwa Asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi.
Kwararrun likita suka tabbatar da cewa magidanci ya rasa ransa ne sakamakon raunukan da ya samu a ƙirjinsa, yayin da wacce ake zargi ta ji kananan rauni a ciki.
Abinda ya faru tun farko tsakanin ma'auratan?
"A binciken da muka yi na farko mun gano cewa Maimuna ta soka wa mijinta Aliyu Muhammed Wuƙa bayan wani ɗan saɓani ya shiga tsakaninsu a cikin gida ranar 5 ga watan Yuli."
"Maimuna ta amsa laifin kashe mijinta yayin bincike. Kwamishinan yan sanda ya bada umarnin miƙa Kes din sashin manyan laifuka domin gudanar da bincike mai zurfi."
- inji ASP Aminu Gimba Ahmed.
Kakakin yan sandan ya ce a halin yanzu ana kan bincike kuma nan gaba kaɗan za'a gurfanar da wacce ake zargi gaban Kotu, kamar yadda rahoton Vanguard ya tattaro.
'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Sun Harbi Mutum 2
A wani labarin na daban kuma Wasu 'yan fashi ɗauke da bindigu sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, da yammacin ranar Talata.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun biyo hadimin masarautar tun daga bankin da ya ciro kuɗi har zuwa bakin kofar shiga fada.
Asali: Legit.ng