Dalibar Da Ta Fi Kowa Maki a Jarabawar JAMB Kamsiyochukwu Umeh Ta Samu Kyautar miliyan 2.5

Dalibar Da Ta Fi Kowa Maki a Jarabawar JAMB Kamsiyochukwu Umeh Ta Samu Kyautar miliyan 2.5

  • Kamsiyochukwu Umeh, ɗalibar da ta fi kowa maki a jarabawar JAMB ta bana, ta samu kyautar kuɗi har naira miliyan 2.5
  • Umeh wacce ɗalibar makarantar 'Deeper Life High School' da ke jihar Ogun ce, ta samu kyautar kuɗin ne daga kamfanin 'Erisco Foods Limited'
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan wata ɗaliba Mmesoma da ta yi iƙirarin fin kowa maki a baya

Ikeja, Legas - An bai wa Kamsiyochukwu Umeh, ɗalibar da ta fi kowa maki a jarabawar JAMB ta bana kyautar kuɗi har naira miliyan 2.5.

Shugaban 'Erisco Foods Limited', kamfanin da ke samar da kayayyakin girke-girke, Dakta Eric Umeofia ne ya ba da kyautar kuɗaɗen ga dalibar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Dalibar da ta fi kowa maki a jarabawar JAMB
Dalibar da ta fi kowa maki a JAMB ta samu kyauta kudi har miliyan 2.5. Hoto: Deeper Life High School
Asali: Facebook

Nawa ɗalibar da ta fi ko maki a jarabawar JAMB ta samu?

Kara karanta wannan

Da Sauran Rina: Abba Kyari Zai Cigaba Da Zama Gidan Yari Duk Da Samun Beli, Bayanai Sun Fito

Umeh, wacce ɗaliba ce a makarantar Deeper Life High School da ke Mowe jihar Ogun, ta samu maki 360 a cikin 400 a jarabawar JAMB da aka yi ta bana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalibar dai ta samu maki 99 a kimiyyar sinadarai (Chemistry), ta samu 98 a lissafi (Mathematics), 97 a kimiyyar Fiziks (Physics), sai kuma ta ci 66 a Turanci (English).

Da yake zantawa da manema labarai, Mista Eric ya ce ɗalibar ta yi matuƙar burge shi ne a hira da ya ga 'yan jarida sun yi da ita.

An yi alƙawarin ba da kuɗaɗe ga makarantar da ɗalibar da ta fi kowa maki a JAMB ta fito

Dan kasuwar bai tsaya iya nan ba, yayin da ya yi alƙawarin bai wa makarantar da dalibar take kyautar kuɗaɗe, haɗi da malaman da suka ɗauke waɗannan darussa guda huɗu.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Jam'iyyar APC Ta Tsoma Baki Kan Bidiyon Dala, Ta Aike da Sako Ga Ganduje

A baya jaridar The Cable ta yi rahoto kan wata ɗaliba mai suna Mmesoma Ejikeme, wacce ta yi iƙirarin cewa ta samu maki 362 a jarabawar ta JAMB da ta rubuta.

Sai dai hakan ya bar baya da ƙura yayin da hukumar shiryar jarabawar ta musanta iƙirarin na ta, wanda hakan ya sanya gwamnatin jihar da ɗalibar ta fito wato Anambra, ba da umarnin a gudanar da bincike.

JAMB za ta fara barin ɗalibai su je ɗakin jarabawa da wayoyinsu

Legit.ng a baya dai ta kawo muku wani rahoto cewa hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB), ta bayyana cewa za ta sahhalewa ɗalibai shiga ɗakin jarabawa da wayoyinsu na hannu.

Hakan a cewar hukumar, zai taimaka ma ta wajen rage yawan kuɗaɗen da take kashewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng