Kano: Rundunar 'Yan Sanda Ta Karyata Jita-Jitar Kashe Jami'inta, Ta Bayyana Abinda Ya Faru

Kano: Rundunar 'Yan Sanda Ta Karyata Jita-Jitar Kashe Jami'inta, Ta Bayyana Abinda Ya Faru

  • Hukumar 'yan sanda a jihar Kano ta musanta zargin cewa an kashe daya daga cikin jami'anta
  • Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a yau Juma'a
  • Ya ce jami'in dan sandan ya samu rauni ne a kai kuma yanzu an sallamo shi daga asibitin Murtala

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta musanta rade-radin cewa an kashe dan sanda a ranar Talata 4 ga watan Yuli yayin gumurzu da 'yan ta'adda.

Hukumar ta ce dan sandan ya samu raunuka ne yayin gumurzun a kasuwar Rimi a ranar Talata 4 ga watan Yuli.

Yan Sandan Najeriya
Jami'in mu bai mutu a Kano ba, Rundunar Yan Sanda. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakikin hukumar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu ta muryar sakon karta kwana, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Abokin Kowa': 'Yan Sandan Kano Za Su Buga Wasan Kwallo Na Sada Zumunta Da Tubabbun 'Yan Daba

Rundunar ta bayyana yadda abin ya faru, inda ta karyata jita-jitar

Ya ce jami'ansu sun isa wurin da ake rikicin ne don kwantar da tarzoma inda daya daga cikinsu ya samu raunuka.

Wani shaidan gani da ido a ranar ya tabbatar da kashe dan sandan, cewar rahotanni.

Amma rundunar ta musanta hakan inda ta ce:

"A ranar 4 ga watan Yuli, da misalin karfe 11 na rana muka samu rahoton cewa wasu 'yan ta'adda na fada a kasuwar Rimi inda suke kokarin kai hari kan mutane.
"Bayan samun rahoton, jami'a mu sun tura 'yan sanda inda aka kama wasu da ake zargi guda bakwai yayin da jami'in mu daya ya samu rauni a kai.
"An kwashe shi zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano inda aka ba shi kulawa kuma aka sallame shi."

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin ci gaba da binciken sirri

Kara karanta wannan

'Na Gaji Da Dawainiya': Matar Aure Ta Nemi Saki Bayan Daukar Nauyin Mijinta Shekaru 10

Ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar ya umarci kwasan wadanda ake zargin zuwa ofishin binciken laifuffuka don gudanar da binciken sirri.

Ya ce bayan kammala binciken za a tura wadanda ake zargin zuwa kotu don hukunta su.

Jami'an Yan Sanda Zasu Buga Wasan Kwallo da Tubabbun 'Yan Daba a Kano

A wani labarin, jami'an 'yan sanda za su buga wasan kwallon kafa don sada zumunci da tubabbun 'yan ta'adda a jihar Kano.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel shi ya tabbatar da haka don tabbatar da tuban su na gaskiya da fatan za su kaucewa aikata laifuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.