'Threads': Kamfanin Twitter Na Shirin Maka Meta A Kotu Kan Zargin Satar Bayanai, Zuckerberg Ya Musanta Zargin

'Threads': Kamfanin Twitter Na Shirin Maka Meta A Kotu Kan Zargin Satar Bayanai, Zuckerberg Ya Musanta Zargin

  • Kamfanin Twitter zai shiga kafar wando daya da kamfanin Meta bisa zargin satar bayanai yayin kirkirar Threads
  • Wannan na zuwa ne bayan kamfanin Meta ya kirkiro sabuwar manhajar 'Threads' mai kama da Twitter a wannan mako
  • Lauyan Twitter, Alex Spiro ya ce suna zargin kamfanin Meta da kutse tare da satar bayanan kamfanin ba tare da izini ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kamfanin Twitter ya yi barazanar maka takwaransa na Meta a kotu saboda yi masa kishiya bayan kirkirar manhajar 'Threads'.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lauyan kamfanin Twitter, Alex Spiro shi ya rubuta takardar koke ga shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg wanda shi ne ya mallaki manhajar 'Threads'.

'Threads': Twitter Na Shirin Maka Meta A Kotu Bisa Zargin Satar Bayanai, Zuckerberg Ya Musa Zargin
Tun Bayan Kirkirar Manhajar 'Threads' Ake Samun Cece-kuce Tsakanin Twitter Da Meta. Hoto: NPR.
Asali: UGC

Kamfanin Meta ya kirkiro manhajar 'Threads' a ranar Laraba 5 ga watan Yuli inda cikin kankanin lokaci mutane fiye da miliyan 30 suka yi rijista.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Zargi Muhammadu Buhari, Sanatoci Za Su Binciki Tsohuwar Gwamnati

Twitter na zargin Meta da kutse ba tare da izini ba

Hakan barazana ne ga Elon Musk mai kamfanin Twitter ganin yadda manhajar 'Threads' ta samu karbuwa saboda yawan mutanen da ke amfani da manhajar Instagram.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Twitter na zargin Threads da amfani da wasu bayanan sirri na kamfanin da ya sabawa dokokin mallakar manhajar, Daily Trust ta tattaro.

A cewar Spiro:

"Twitter na kokarin kare 'yancin mallakarsa, da bukatar Meta ya daina amfani da sirrukan Twitter ko kuma wasu bayanai da ke bukatar sirrantawa."

Spiro a cikin wata takarda ya zargi Meta da daukar tsoffin ma'aikatan Twitter don ci gaba da kutse a manhajar musamman wadanda suka shafi bayanan sirri.

Meta ya karyata zargin da ake masa kan tsoffin ma'aikatan Twitter

Kakakin kamfanin Meta, Andy Stone ya ce babu wani tsohon ma'aikacin Twitter a rukunin injiniyoyin Threads.

Kara karanta wannan

Har An Fara Murna, Sai AA Rano Ya Musanta Karya Farashin Litar Fetur Daga N540

Ya ce:

"Babu wani daga cikin injiniyoyin Threads wanda tsohon ma'aikacin Twitter ne, wannan ba hujja ba ne."

Wani daga cikin manyan tsoffin ma'aikatan Twitter ya fadawa 'yan jaridu cewa ba su da wata masaniya akan wasu tsoffin ma'aikatan Twitter da ke aiki a Threads, ko kuma wani babban ma'aikaci da ya ke Meta.

Mai kamfanin Twitter, Elon Musk yayin mai da martani ya ce:

"Gasa ta na da kyau, amma zamba babu kyau."

Kamfanin Meta Sun Fatattaki Sama Da Ma’aikata 11,000

A wani labarin, kamfanin Meta wanda ya mallaki manhajar Facebook ya fatattaki ma'aikata sama da 11,000

Rahotanni sun tabbatar cewa yawan wadanda aka koran sun kai kashi 13 na ma'aikatan kamfanin.

Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg shi ya bayyana korar ma'aikatan a sakon da kamfanin ta sake a labaransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.