Yajin Aikin Likitoci Ya Janyo Rasa Ran Mace Mai Juna Biyu Da Jaririnta a Nasarawa

Yajin Aikin Likitoci Ya Janyo Rasa Ran Mace Mai Juna Biyu Da Jaririnta a Nasarawa

  • Wata mata mai juna biyu da jaririn cikinta sun mutu a wani asibitin ƙwararru mallakin gwamnati da ke Lafia
  • An tattaro cewa matar ta rasu ne sakamakon rashin samun likitocin da za su duba ta a asibitin
  • Rahotanni sun ce likitocin sun shiga yajin aikin wucin gadi na kwanaki biyar don yin ƙorafi kan walwalarsu ga gwamnatin jihar

Lafia, jihar Nasarawa - Wani lamari mai ban tausayi ya faru a jihar Nasarawa, inda wata mata mai juna biyu ta mutu a asibitin kwararru wato 'Dalhatu Specialists' mallakin gwamnatin jihar da ke Lafia.

An tattaro cewa matar ta mutu ne sakamakon rashin likitocin da za su duba ta, wnda a halin yanzu suke yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar.

Yajin aiki ya janyo mutuwar mace mai juna biyu a Nasrawa
Yajin aikin likitoci ya janyo mutuwar mace mai juna biyu a jihar Nasarawa. Hoto: STEFAN HEUNIS/AFP
Asali: Getty Images

Yajin aikin likitoci ya hana a yi wa matar aiki

Kara karanta wannan

Hukumar NEMA Ta Kawo Jerin Jihohi 14 Da Za a Fuskanci Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

An ce matar wacce ba a bayyana sunanta ba, an shirya cewa za a yi ma ta tiyata a ranar Talata da ta gabata, sai dai hakan bai samu ba saboda yajin aikin da likitocin ke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar ta rasu bayan rashin gudanar da tiyatar da aka shirya yi mata a lokacin da ya dace.

An kuma bayyana cewa ana kwashe marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta gaggawa zuwa asibitoci masu zaman kansu don ci gaba da samun kulawar likitoci.

Mijin matar da ta rasu ya yi martani kan lamarin

Daily Trust ta ruwaito mijin matar, Malam Abubakar Liman yana cewa, rashin kuɗi ne ya sanya shi kawo matarsa asibitin gwamnati maimakon asibitin kuɗi.

Malam Liman ya bayyana cewa, ta yi wu mutuwar matar tasa da yaron cikin nata haka Allah ya so, sai dai ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta biyawa likitocin buƙatunsu.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mamakon Ruwan Sama Ya Yi Awon Gaba Da Mutane 2 a Birnin Katsina

Shugaban ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Bauchi Dr Attah Peter, ya zagaya asibitin tare da mutanensa don tabbatar da ana bin umarnin yajin aikin da suka ba da.

Bayanai sun nuna cewa likitocin sun ƙaddamar da yajin aikin ne a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli.

PM News ta wallafa cewa an samu raguwar mutane sosai a asibitin, sakamakon yajin aikin da ke gudana.

Likitoci sun raba jarirai biyu da aka haifa tare a jihar Adamawa

A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta yadda wasu likitoci a jihar Adamawa suka raba jarirai biyu da aka haifa manne da juna.

An bayyana cewa manyan likitoci da dama ne suka haɗu wajen yin aikin raba 'yan biyun da suka kasance duka mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng