Gwamnatin Kwara Ta Soke Matakin Rage Ranakun Aiki Daga 5 Zuwa 3

Gwamnatin Kwara Ta Soke Matakin Rage Ranakun Aiki Daga 5 Zuwa 3

  • Gwamnatin jihar Kwara ta janye matakin rage wa ma'aikatanta kwanakin zuwa wurin aiki daga kwana 5 zuwa 3
  • A sabon umarnin da gwamnatin ta bayar, ta ce kowane ma'aikaci zai koma zuwa wurin aiki tsawon kwanaki 5 a mako kamar yadda aka saba
  • Gwamnatin ta lashe amanta ne sabida bai wa gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin gwadugo damar aiki kan rage raɗaɗin cire tallafin mai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kwara - Gwamnatin jihar Kwara karkashin gwamna Abdulrahman Abdulrazak ta janye shirin rage ranakun aiki ga ma'aikata daga kwanaki 5 zuwa 3.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a ranar 5 ga watan Yuni, 2023, gwamnatin Kwara ta sanar da rage wa ma'aikatan jihar ranakun zuwa wurin aiki daga kwana 5 zuwa 3.

Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazak.
Gwamnatin Kwara Ta Soke Matakin Rage Ranakun Aiki Daga 5 Zuwa 3 Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Asali: Twitter

Wannan mataki ya fito daga ofishin shugabar ma'aikatan jihar, Misis Susan Oluwole.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Haramta ‘Gasar Kiss’, Ta Gargadi Masu Neman Kawo Rashin Tarbiyya a Ekiti

Ta ce gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin rage wa ma'aikatan raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin Kwara ta janye wannan garabasa

A wata takarda da ta aike wa shugabannin ma'aikatu, sashi-sashi da hukumomin gwamnatin jihar Kwara, Misis Oluwole ta ce an janye wannan garaɓasa.

A cewar shugabar ma'aikatan, a yanzu kowane ma'aikaci zai ci gaba da zuwa wurin aiki na tsawon kwanaki 5 a mako kamar yadda aka saba a baya.

Ta ce gwamnati ta janye rage kwanakin da ta yi ne sabida bai wa FG da ƙungiyoyin kwadugo cikakkiyar dama da zasu yi aikin lalubo hanyar rage wa mutane zafin cire tallafin.

Takardar mai dauke da sa hannun shugaban sashin ayyuka, Mista Okedare Adeyinka, ta ce nan ba da jimawa ba tallafin rage raɗaɗin zai riski al'umma.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Gwamnatin Jihar APC? Gaskiya Ta Bayyana

"An umarce ni na sanar da dukkan shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnati cewa an janye matakin rage kwanakin aiki."
"Saboda haka ma'aikata na kowane rukuni zasu koma zuwa aiki tsawon kwanaki 5 a kowane mako kamar yadda aka saba daga ranar 10 ga watan Yuli, 2023."
"Haka nan ma'aikatan da a wancan lokacin ba su ci gajiyar rage ranakun aikin ba zasu samu ƙunshin wani tallafin kuɗi domin nuna yabo da godiya."

Malaman makaranta, ma'aikatan lafiya da sauran wasu ma'aikata da ke aiki mai matuƙar muhimmanci ba su ci gajiyar rage ranakun ba saboda yanayin aikinsu.

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Ƙasa da Sakatare a Villa

A wani rahoton na daban kuma Shugaba Tinubu ya gana yanzu da shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da sakatare, Iyiola Omisore a Aso Rock.

Jiga-jigan biyu sun dira fadar shugaban ƙasa mintuna kalilan kafin ƙarfe 5:00 na yamma ta cika ranar Laraba, 5 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Kakaba Wa Dalibai Harshen China A Jami'o'i, Ta Roki Alfarma

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262