Cire Tallafin Mai: Gwamna Kefas Na Taraba Ya Ragewa Daliban Jami'a Kudi Da Kaso 50% a Jihar

Cire Tallafin Mai: Gwamna Kefas Na Taraba Ya Ragewa Daliban Jami'a Kudi Da Kaso 50% a Jihar

  • Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya sanar da rage kuɗaɗen makarantar ɗaliban jami'ar jihar Taraba da kaso 50%
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne saboda rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa mutanen jihar a ciki
  • Ɗalibai da iyayensu sun yi godiya gami da nuna matuƙar farin cikinsu da gagarumin matakin da gwamnan ya ɗauka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ba da umarnin a yi gaggawar ragewa ɗaliban jami'ar jihar kuɗaɗen makaranta da kaso 50%.

Ya ba da umarnin ne a yayin wata ziyara ta ba zata da ya kai makarantar don duba halin da ta ke ciki, kamar yadda Channels TV ta wallafa.

Kefas ya ragewa daliban jihar Taraba yawan kudin makaranta
Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya rage kudin makaranta da kaso 50%. Hoto: Agbu Kefas
Asali: Facebook

Cire tallafin man fetur ne ya sa aka rage kuɗin makarantar

Gwamnan ya ce ya yanke hukuncin ne sakamakon cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi, wanda ka iya hana wasu ɗaliban biyan kuɗin makaranta.

Kara karanta wannan

Jerin Muhimman Tambayoyin da Ya Zama Tilas JAMB Ta Amsa Kan Ɗalibar da Ake Zargi Da Ƙara Yawan Maki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin ziyarar, gwamnan ya gano cewa akwai kwasa-kwasai 53 na makarantar da ba a tantance ba.

Hakanan gwamnan ya gano cewa an samu ƙarin kuɗin makaranta da kuma rashin ingantaccen wurin kwanan ɗalibai.

Sannan gwamnan ya kuma buƙaci ba'asi kan abinda ke hana ɗaliban makarantar zuwa bautar ƙasa ta NYSC, ko kuma makarantar horar da lauyoyi yayin da suka kammala digirinsu a nan.

Ɗalibai da iyayensu sun nuna farin cikin da rage kuɗin makarantar da Kefas ya yi

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ɗaliban makarantar sun nuna matuƙar farin cikinsu da rage kuɗaɗen makarantar da gwamnan ya yi. Sun ce hakan zai taimaki rayuwarsu sosai.

A nasu ɓangaren, iyayen yara sun yaba da wannan mataki da gwamnan ya ɗauka, inda suka ce dama cire tallafin man fetur da aka yi, ya jefasu cikin yanayin da biyan kudin makarantar ke musu wahala.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mamakon Ruwan Sama Ya Yi Awon Gaba Da Mutane 2 a Birnin Katsina

Gwamna Kefas zai binciki abubuwan da suka faru a shekaru 4 na baya a jihar Taraba

Legit.ng ta kawo muku rahoto a baya kan cewa gwamnan jihar ta Taraba, Agbu Kefas, ya kafa kwamitin da zai binciki duk wasu hukumomin jihar kan yadda suka tafiyar da ofisoshinsu daga 2019 zuwa 2023.

Hakan ya biyo bayan sauke shugabannin duk wasu ma'aikatun jihar da tsohon gwamna, Darius Ishaku ya naɗa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng