Kotu Ta Tsare Wani Matashi Kan Zargin Satar Jaririya ’Yar Watanni 2, Ya Yi Ikirarin ’Yarsa Ce

Kotu Ta Tsare Wani Matashi Kan Zargin Satar Jaririya ’Yar Watanni 2, Ya Yi Ikirarin ’Yarsa Ce

  • Wata kotun majistare da ke zamanta a Yenagoa ta jihar Bayelsa ta tsare wani matashi bisa zargin cin zarafi da kuma sata
  • Ana zargin matashin Kingsley Solomon da satar jaririya mai kimanin watanni biyu a duniya mai suna Success a Yenagoa
  • Mai Shari'a, Sarah Awoh ta umarci tsare shi na kwanaki 15 bayan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bayelsa - Kotun majistare da ke zamanta a Yenagoa cikin jihar Bayelsa ta tsare wani matashi a gidan kaso bisa zargin satar jariririya.

Matashin, Kingsley Solomon mai shekaru 30 ana zarginshi da satar jaririya da ba ta wuce watanni biyu ba a yankin Azikoro da ke birnin Yenagoa.

Kotu Ta Tsare Wani Matashi Kan Zargin Satar Jaririya ’Yar Watanni 2
Kotu Ta Tsare Matashi Bisa Zargin Satar Jaririya. Hoto: Facebbok.
Asali: Facebook

Tun farko mai gabatar da kara ya ce a ranar 23 ga watan Yuni, Solomon ya naushi wata mata mai suna Joy Lucky a gefen idonta da niyyar sayar jaririya wanda hakan ya sabawa dokar jihar sashe na 282.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Shafe Watanni 4 a Otel Din Alfarma, Matashi Ya Ajiye Cak Din Miliyan 12 Na Bogi Sannan Ya Tsere

Ana zargin matashin da sace jaririya mai watanni biyu

Ya kara da cewa, Solomon a ranar 24 ga watan Yuni ya sace jaririyar mai suna Success Alfred 'ya ga Joy Lucky 'yar kimanin watanni biyu wanda hakan har Ila yau, ya sabawa doka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahotanni sun tabbatar da cewa Solomon ya yi ikirarin cewa sun yi mu'amala da Joy a otal, amma ya tabbata ba jaririyarsa ba ce.

Solomon ya musanta zarginsa da ake kan cin zarafi da kuma sata, Daily Trust ta tattaro.

Kotun ta ba da umarnin ci gaba da tsare matashin a gidan kaso

Mai Shari'a, Sarah B. I Awoh ta umarci a tsare Solomon har tsawon kwanaki 15.

Idan ba a mantaba, rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ta kama Solomon da taimakon Eunice Nnaci ta hukumar kare hakkin mata (ENWAF) bayan samun rahoton satar jaririyar Joy mai suna Success.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya Ya ba Ministar Shugaba Buhari Aiki Daga Barin Gwamnatin Najeriya

Jami'an 'Yan Sanda Sun Kama Ma'aikatan Jinya 2 Da Mai Gadin Asibiti Kan Zargin Satar Mabiyiya

A wani labarin, jami'an 'yan sanda sun yi nasarar cafke wasu ma'aikatan jinya biyu bisa zargin satar mabiyiya.

Sannan cikin wadanda aka kaman akwai mai gadin asibitin da suka hada baki don aikata wannan ta'asa.

Rindunar 'yan sanda ta ce wadanda aka kaman suna aiki ne a cibiyar lafiya ta Comprehensive da ke Owo cikin jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel