Asiri Ya Tonu: An Kama Waɗanda Suka Kulla Garkuwa da Babban Malamin Musulunci

Asiri Ya Tonu: An Kama Waɗanda Suka Kulla Garkuwa da Babban Malamin Musulunci

  • 'Yan sanda sun kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a garkuwa da babban Malamin Musulunci na garin Uso a jihar Ondo
  • Hukumar 'yan sanda ta nuna waɗanda ta kama wanda suka ƙunshi maza biyu da mace guda ɗaya ranar Talata
  • Macen mai suna Aisha Belle ta musanta hannu a aikata laifin, ta ce ɗaya daga ciki ne ya zo ya ari layin wayarta

Ondo state - Shugaban tawagar masu garkuwa da mutane da abokan aikinsa 2 sun shiga hannu bisa zargin sace babban limamin garin Uso a ƙaramar hukumar Owo, jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade.

Idan baku manta ba wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da Malamin a gonarsa da ke sansanin Asolo, yankin Uso watan da ya gabata.

An kama masu hannu a sace Limami a Ondo.
Asiri Ya Tonu: An Kama Waɗanda Suka Kulla Garkuwa da Babban Malamin Musulunci Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa daga baya Malamin ɗan kimanin shekara 67 a duniya ya kubuta daga hannun maharan bayan biyan miliyan N2 a matsayin kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Fadar Sarkin Minna Wuta Kuma Yana Ciki, Sun Tafka Ta'adi

'Yan sanda sun kama mutum 3 bisa zargin sace Limamin

A halin yanzu, 'yan sanda sun damƙe shugaban masu garkuwan, Muinah Mohammed, ɗan shekara 19 da yaransa biyu da ake zargi, Aisha Bello, 20 da Isah Bello, 40 bisa zargin garkuwa da Malamin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta nuna waɗanda ake zargin a hedkwatar 'yan sanda da ke Akure ranar Talata.

Ta ce dakaru sun samu nasarar cafke waɗanda ake zargin bayan matar babban Malamin ta kai wa yan sanda rahoton yadda aka sace mijinta a gona.

Ta ce:

"Nan take bayan samun rahoton Kes din, jami'an yan sanda suka bazama bincike kuma a karshe Malamain ya kubuta amma ta hanyar fasaha da bayanan sirri muka kama waɗanda ake zargi."

Kakakn 'yan sandan ta ƙara da cewa wayar salulan da aka yi amfani da ita wajen tattauna kuɗin fansar da iyalai suka biya, yan sanda sun ganota a tare da wanda ake zargi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Buhari a Villa, Yan Najeriya Sun Nuna Damuwa

Ta ce nan ba da jimawa ba hukumar 'yan sanda zata gurfanar da mutanen uku gaban Kotu bayan kammala bincike, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Bani da hannu a sace mutumin - Aisha Bello

Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, Aisha Bello, ta ce ko kusa bata da hannu a garkuwa da malamin. Ta ce Muhammed ya zo wurinta ya ari layi zai yi kira amma tun lokacin ta bar masa layin.

Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Fadar Sarkin Minna Wuta Kuma Yana Ciki, Sun Tafka Ta'adi

A wani labarin na daban kuma Yan fashi sun aikata ta'adi ido na ganin ido a fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, ranar Talata.

An ce ɗaya daga cikin masu yi wa fadar hidima da aka aika banki domin ya ciro kuɗi 'yan bindigan suka biyo a wata mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262