Masallacin Annabi Muhammad SAW Ya Karbi Bakuncin Masu Kai Ziyara 4.25 a Mako Daya

Masallacin Annabi Muhammad SAW Ya Karbi Bakuncin Masu Kai Ziyara 4.25 a Mako Daya

  • Hukumar kula da Masallacin Nabwi da ke birnin Madina ta fitar da rahoton ayyukan tsakanin 7 zuwa 14 ga watan Dhul-Hijjah 1444
  • Rahoton ya nuna cewa Musulmai sama da miliyan 4.2 ne suka kai ziyara Masallacin Annabi Muhammad SAW a cikin mako 1
  • An kuma yi tanadi mai kyau ga masu ziyara da masu zuwa ibada, haka zalika an raba kyaututtuka da ruwan Zamzam

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hukumar da ke jagorantar kula da masallacin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ta fitar da rahoton ziyarar da aka kai Masallacin cikin mako ɗaya.

Ta ce Masallaci ya karɓi bakuncin Musulamai miliyan 4,252,000 da masu kai ziyara daban-daban a tsakanin 7 zuwa 14 ga watan Dhul Hijjah wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

Masallacin Annabi Muhammad SAW.
Masallacin Annabi Muhammad SAW Ya Karbi Bakunci Masu Kai Ziyara 4.25 a Mako Daya Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Facebook

A rahoton mako-mako, mahukuntan Masallacin mai alfarma sun nuna irin kyakkyawan tanadin da aka yi domin masu ibada da masu kawo ziyara Masallacin Manzon Allah (SAW).

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar Masallacin ta haɗa kai da hukumomin tsaro, lafiya, ayyuka, bada agajin gaggawa da 'yan sa'kai domin tabbatar da komai ya tafi bisa tsari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ayyukan da aka gudanar fisabilillah a Masallacin Nabwi

Mahukuntan Masallacin sun bayyana a rahoton cewa sun shirya da saukaka wa mutane 271,173 masu ziyara domin gaida fiyayyen halitta tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi.

Wannan adadi ƙari ne kan masu ibada 75,529 da aka amince su ziyarci Rawdah Sharif.

"Tsofaffi sama da 6,782 suka amfana da wuraren da aka tanada domin mutanen da shekarunsu suka ja yayin da masu kai ziyara 14,766 suka saurari karatun Addinin Musulunci a Masallacin Annabi SAW."

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Gangwaje Alhazan Jihar Kano, Ya Ba Su Kyautar Miliyan 65

Hukumar ta ƙara da cewa ta raba kyaututtuka daban-daban guda 46,138 a tsakanin Alhazai da kuma masu zuwa ibada Masallacin.

Haka zalika ta ce an raba kwalaben ruwan Zamzam 203,294 da kuma ƙunshin abinci 426,457 ga waɗanda ke Azumi.

Gwamna Radda Ya Gwangwaje Alhazan Katsina da Kyautar Miliyan N278m

A wani labarin na daban kuma Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bai wa alhazan jihar Katsina tallafin kuɗi miliyan N278m a Saudiyya.

Shugaban Alhazan jihar Katsina (Amirul Hajj), Alhaji Tasiu Musa-Maigari, shi ne ya tabbatar da haka a Makkah ranar Lahadi yayin da ya ziyarci alhazan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262