Dami a Kala: An Turo Wa Wani Mutumi Sama da Biliyan N24bn a Asusun Banki

Dami a Kala: An Turo Wa Wani Mutumi Sama da Biliyan N24bn a Asusun Banki

  • Ana tuhumar wani mutumi bisa zargin satar zaune bayan kashe miliyan N750m da banki ya tura asusunsa bisa kuskure
  • Bankin ya yi kuskuren sanya kuɗi biliyan N24bn a asusun mutumin bisa kuskure sakamakon wata 'yar tangarɗa
  • Jami'an yaƙi da masu zamba ne suka damƙe mutumin kuma sun samu nasarar kwato tsabar kuɗi naira miliyan N450m a cikin gidansa

Wani mutumi mai suna Joel Julien daga Trinidad ya shiga hannun jami'ai bisa zargin sace makudan kuɗi daga bankinsa bayan tafka babban kuskure.

Bisa tsautsayi, bankin ya antaya kudi sama da biliyan N24bn a asusun mutumin amma ganin tamkar ya tsinci dami a kala, mutumin ya ci gaba da sha'aninsa da kuɗin.

Yadda wani mutumi ya kashe kuɗin da ba nasa ba.
Dami a Kala: An Turo Wa Wani Mutumi Sama da Biliyan N24bn a Asusun Banki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A rahoton da Jamian Observer ta tattara, kafin Mista Julien ya shiga hannu, har ya yi shagalinsa da miliyan N750m daga cikin zunzurutun kuɗin da aka tura masa bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Rabu Da Mijinta Bayan Ta Samu N1.5bn, Kotu Ta Umarci Ta Ba Mijin Duka Kudin, Ta Bayar Da Kwakkwaran Dalili 1

Za'a gurfanar da mutumin gaban Kotu ya yi bayani

A halin yanzu jami'an 'yan sanda na tuhumar Julien da satar zaune kuma zai gurfana gaban Kotu domin ya yi bayanin dalilin da ya sa ya taɓa kuɗin da ba na shi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A rahoton Guardian, yan sanda sun gano cewa bankin ya fahimci kuskuren da ya tafka ne bayan nazari kan bayanan ayyukan da suka gudana.

Sun gano cewa tangarɗar da na'urarsu ta samu ya yi sanadin tura kuɗi dala 32,347,308.55 zuwa asusun Julien.

Yan sanda sun ce Julien ya yi amfani da kuɗin ta hanyar zuwa na'urar ATM ya zare tsabar kuɗi da kuma amfani da katinsa wajen sayayya a shaguna.

Mutumin ya kashe miliyan N750m daga cikin kuɗin a tsakanin 18 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, inji yan sanda.

Kara karanta wannan

"Ina Kaunar Mijina Duk da Yana Bugu Na Kamar Jaka" Wata Mata Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci, Ta Gindaya Sharaɗi 1

Meyasa ya ƙi maida kuɗin?

Bankin ya yi ƙoƙarin dawo da kuɗin daga hannun Julien ta hanyar maslaha amma ya ƙi ba da haɗin kai, bisa haka ya kai ƙararsa ga jami'an yaƙi da zamba.

Yayin bincike jami'an suka yi ram da Julien kuma suka kwato tsabar kuɗi dala 600,501 a cikin gidansa.

Gwamna Radda Ya Gwangwaje Alhazan Katsina da Kyautar Miliyan N278m

A wani labarin na daban kuma Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bai wa alhazan jihar Katsina tallafin kuɗi miliyan N278m a Saudiyya.

Shugaban Alhazan jihar Katsina (Amirul Hajj), Alhaji Tasiu Musa-Maigari, shi ne ya tabbatar da haka a Makkah ranar Lahadi yayin da ya ziyarci alhazan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262