Tinubu Ya Tsokano ‘Yan ASUU a Wajen Tsige Duka Shugabannin Hukumomin Gwamnati
- Bola Ahmed Tinubu ya bi majalisun da ke kula da jami’o’in Gwamnatin tarayya, duka ya sauke su
- Malaman jami’a a karkashin kungiyarsu ta ASUU sun yi tir da wannan lamari, sun ce an saba doka
- An zargi Gwamnatin tarayya da kawowa sha’anin ilmin jami’a matsala, ana bukatar ta sauya zani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta soki gwamnatin tarayya a dalilin sauke duka majalisar shugabannin da ke sa ido a kan harkokinsu.
Bola Ahmed Tinubu ya sauke majalisun da ke kula da jami’o’in gwamnatin tarayya, Premium Times ta ce hakan ya jawowa Gwamnatinsa suka.
Da aka yi hira da shugaban kungiyar ASUU na reshen jami’ar Jos, Chris Yilgwan, ya caccaki wannan mataki da aka dauka, ya ce zai jawo matsaloli.
Gwamnatin tarayya tayi amfani da hukumar NUC wajen tsige wadannan majalisu, Dr. Chris Yilgwan ya ce yin hakan zai gurguanta jami’o’i ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake zantawa da hukumar dillacin labarai, Yilgwan ya nuna bai dace a cigaba da tafiya a haka ba.
Gwamnati ta saba dokokin kasa
Malamin jami’ar ya nuna an saba doka wajen sauke wadannan majalisu, The Cable ta rahoto shi ya na ba gwamnatin Tinubu shawara ta sake nazari.
"Ruguza shugabannin da ke sa ido a kan harkokin jami’ar gwamnatin tarayya da NUC tayi kwanan-nan ya ci karo da dokar 2003 da aka yi wa kwaskwarima.
Dokar ta ba shugabannin majalisun jami’o’in wa’adin da za su shafe, saboda haka ba za a iya wargaza su tamkar sauran shugabannin hukumomi ba.
Majalisar da ke kula da jamio’i ita ce mafi girman hukuma a kowace jami’a, da zarar an ruguza ta ba tare da maye gurbinta, an tsaida komai cak a jami’a.
Saboda haka mu na daukar ruguzawar a matsayin tasgaro ga cigaban karatun jami’a, kuma mu na kira ga gwamnatin tarayya ta canza matakin da ta dauka.”
- Dr. Chris Yilgwan
Jaridar ta ce Yilgwan ya nemi gwamnati ta zama mai bin doka a abubuwan da su ka shafi jami’o’i.
Harajin POC zai tatso N12bn
Rahoto ya zo cewa harajin POC da za a fara biya a bana zai jawo gwamnati ta samu kusan Naira biliyan 12 domin akwai motoci fiye da miliyan 12 a titi.
Idan mafi yawan masu motoci, gingimari, babura da keke napep su ka yi biyayya, za a samu Biliyoyi, sai dai jama’a da-dama sun soki wannan sabon tsari.
Asali: Legit.ng