An Samu Labarin Abin da Bola Tinubu Ya Fadawa Sababbin Hafsun Tsaro a Aso Villa

An Samu Labarin Abin da Bola Tinubu Ya Fadawa Sababbin Hafsun Tsaro a Aso Villa

  • Nuhu Ribadu ya yi bayanin abin da su ka tattauna da su ka sa-labule da Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock
  • A mai bada shawara kan harkokin tsaro ya ce sun samu lokaci sun yi wa shugaban Najeriya godiya
  • Malam Ribadu ya yi alkawarin cewa shi da takwarorinsa ba su yi kasa-a-gwiwa wajen tsare kasar nan

Abuja - Mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana wainar da aka toya da su ka hadu da Bola Ahmed Tinubu.

A yammacin Litinin, Daily Trust ta rahoto Malam Nuhu Ribadu ya na cewa sun yi amfani da damar da su ka samu wajen godewa shugaban kasa.

Ganin ya nada su domin su hidimtawa kasarsu, Ribadu ya shaida cewa sun yi godiya tare da yi wa Mai girma Bola Tinubu alkawarin yi masa biyayya.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida Ya Soke Karin Girman Da Ganduje Ya Yi Wa Malaman Makaranta

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Hafsoshin Tsaro Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

NSA: "Abin da ya kawo mu"

“Mun zo ne domin godewa shugaban kasa na damar da ya ba mu na bautawa kasarmu kuma mu yi wa gwamnatinsa hidima.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mun tabbatar da biyayyarmu a gare shi da Najeriya da mutanen Najeriya. Mun yi imani cewa ya dauki matakin da ya kamata.

- Nuhu Ribadu

A matsayinsa na NSA, Malam Ribadu ya ce sun san abin da shugaba Tinubu ya ke so ga kasar nan.

Shugaba Tinubu yana tare da mu

"Za mu yi aiki babu kaukautawa domin cin ma wannan manufa na kare kasarmu, kawo tsaro da zaman lafiya da kare rayuka.

Ya yi mana alwashin ya na tare da mu dari-bisa-dari. Ya kuma fada mana dole mu yi aiki tare kuma akwai aikin da ke gabanmu.
Ya (Tinubu) ya fada mana ya na sa ran mu sauke nauye-nauyenmu da kyau kuma mu na gode masa, abin da ya kawo mu kenan."

Kara karanta wannan

Abu namu: Buhari ya tura wa Tinubu sunan wanda yake so a ba Minista daga Katsina

- Nuhu Ribadu

An fara samun tsaro a Najeriya

An rahoto tsohon ‘dan sandan ya na cewa an fara samun saukin rashin tsaro, ya ce laifuffuka sun ragu, ya na mai fatan adadin ta’adin da ake yi ya sauka.

A cewar Ribadu, hafsoshin tsaron da aka zabo su na cikin zakarun da ake da su, saboda haka yake alkawarin ba za su bada kunya wajen inganta tsaro ba.

An yi canjin shugabanni a soja

Rahoto ya zo cewa zaman Manjo Janar Taoreed Lagbaja Shugaban Hafsun Sojojin Kasa a watan Yunin da ya gabata ya kawo wasu sauye-sauye a gidan soja.

Za a nada wasu sababbin Birgediya Janar, Manjo Janar, Rear admirals da Air Vice Marshall a Najeriya domin su rike mukaman da magabatansu za su bari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng